Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu

Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ta amince da fitar da Naira Biliyan 108 don gini da gyaran tituna guda hudu.

Za a gudanar da ayyukan titin ne a jihohin Adamawa, Borno, Enugu da Rivers kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja bayan taron na FEC da aka gudanar a ranar Laraba.

Ya ce majalisar ta amince a kara ware Naira Biliyan 25 akan kwangilolin da aka bayar a baya domin karasa sashin Lokponta na babban titin Enugu zuwa Port Harcourt.

Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu
Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu. Hoto daga Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Fashola ya ce, "Maaikatan Ayyuka da Gidaje ta gabatar da batutuwa guda biyu.

"Na farko shine tallafin neman karasa aikin sashin Lokponta na babban titin Enugu zuwa Port Harcourt.

"Ana neman karin Naira Biliyan 25 don karasa wani kwangila da aka fara kuma majalisar ta amince da hakan.

Ministan ya kuma ce Majalisar ta amince da bayar da kwangilar ayyukan wasu tituna uku daban.

"Na farkon shine titin Dikwa-Marte-Monguno a kan kudi Naira Biliyan 60.273 da titin Numan da ke sada Borno da Adamawa a kan Naira Biliyan 15.527.

"Na ukun shine titin Gombi-Biu da ke sada Adamawa da Borno a kan kudi Naira Biliyan 7.643."

A bangaren Ilimi, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana cewa za a yi wa dakunan kwanan daliban Kwallejin Fasaha ta Kaduna, Kaduna polytechnic, gyara.

Ya ce wani mai saka hannun jari ne ya bayar da kudi N774,264,000 don yin gyaran.

Ya tabbatar wa daliban kwallejin cewa gyaran ba zai saka ayi musu karin kudin dakunan kwanan ba.

"Za ayi shekara guda ana aikin gina dakunan daliban, bayan an gama dan kwangilar zai rika karbar kudaden haya na shekara 15 inda zai mayar da kudinsa.

"Dalibai 4,032 ne ake sa ran za su samu matsuguni a dakunan kwanan idan an kammala," in ji Mr Adamu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel