An gano gawar mutane 180 a wani kabari a kauyen Djibo

An gano gawar mutane 180 a wani kabari a kauyen Djibo

Kungiyar kare hakkin bil'adama, 'Human Rights Watch' ta ce ta gano wani kabari da aka binne gawarwaki har 180 a arewacin kasar Bukina Faso.

An gano gawarwakin ne a wani babban kabari da ke kauyen Djibo a arewacin kasar Burkina Faso inda sojoji ke yaki da 'yan ta'adda.

Human Rignts Watch ta ce "mu na da hujjojin da ke nuna cewa akwai sa hannun jami'an gwamnati a kisan fararen hula ba bisa ka'ida ba".

An zubar da gawarwakin mutanen ne a wurare daban - daban a kusa da kauyen Djibo kafin daga bisani mazauna garin su tattaresu su binne a wani kabari.

Sai dai, ministan tsaro na kasar Burkina Faso ya bayyana cewa bai kamata a dora alhakin kisan mutanen a kan gwamnatin kasar ba.

A cewarsa, kamata ya yi a dora alhakin kisan mutanen a kan 'yan ta'adda da ke tayar da kayar da baya a yankin.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, bisa rakiyar dumbin dakarun soji, ya sake kaddamar da wani sabon atisaye.

Atsayen mai taken ,Ofireshon Sahel Sanity, an kaddamar da shine ranar Litinin domin magance aiyukan 'yan bindiga a yankin arewa ma so yamma.

Yayin kaddamar da sabon atisayen a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Buratai ya ce an kaddamar da sabon atisayen da sauran wasu a baya domin dawo da zaman lafiya a jihohin yankin arewa ma so yamma da 'yan bindiga su ka addaba.

An gano gawar mutane 180 a wani kabari a kauyen Djibo
Buhari da shugaban kasar Burkina Faso
Asali: UGC

"Rundunar sojin Najeriya za ta gudanar da atisayen Sahel Sanity tare da hadin gwuiwar sauran hukumomin tsaro da suka hada da rundunar 'yan sanda, jami'an tsaron farin kaya (DSS) da gwamnatin.

"A shirye mu ke mu kawar da 'yan bindiga, satar shanu da sauran wasu aiyukan ta'addanci a yankin arewa ma so yamma da arewa ta tsakiya," a cewar Buratai.

DUBA WANNAN: Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda

Sai dai, a yayin da Buratai ke kaddamar da wannan atisaye, wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Yar Gamji mai nisan kilomita 150 daga karamar hukumar Batsari tare da kashe manoma 30 da ke aiki a gonakinsu.

'Yan bindigar, kimanin su 200, sun dira kauyen a kan babura da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Litinin.

Mazauna kauyen sun sanar da jami'an tsaro halin da ake ciki kuma an turo dakarun soji domin bayar da gajin gaggawa.

'Yan bindigar sun gudu zuwa cikin dazukan da suka fito bayan sun dan fafata musayar wuta da jami'an tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel