Kotu ya yanke wa matsafi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun

Kotu ya yanke wa matsafi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun

Wata babban kotu da ke zamanta a Ile-Ife jihar Osun a ranar Talata ta yanke wa wani Oluleke Ogunyemi mai shekara 37 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da aikata kisa.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban kotu a ranar 6 ga watan Maris na 2013 saboda kashe wani Moshood Babalola.

An tuhume shi da laifin hadin baki da kisar gillar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Laifukan sun ci karo da sashi na 319 da 324 na dokar criminal code cap. 34 ta jihar Osun.

An yanke wa matsafi hukuncin kisa ta hanyar rataya
An yanke wa matsafi hukuncin kisa ta hanyar rataya. Hoto daga The Punch
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Boko Haram ta tabbatar da ƙawancenta da ƴan bindigan Niger cikin sabon bidiyo

A cewar bayanan da kotun ta bayar, wanda ake zargin, a unguwar Iredunmi da ke Ile-Ife a ranar 17 ga watan Fabrairun 2010 ya kashe Babalola bayan guntule kansa da wuka.

Mahaifin marigayin, Sikiru Babalola ya kai rahoto a ofishin yan sanda da ke More a Ile-Ife.

A yayin gudanar da shari'ar, lauyan mai shigar da kara daga ma'aikatar shari'a na jihar, Mr Tijani Adekilelekun ya kira shaidu guda biyar.

Da ya ke bayar da shaida a kotu, shaidan wanda ya shigar da kara, Sufeta Rasheedat Olanrewaju ta ce ita da wasu jamian yan sanda biyu sun ziyarci unguwar Agbedegbede inda wanda ake zargin ke zaune.

Ta ce ita da tawagarta yayin bincika gidan wanda ake zargin sun gano gawar wanda abinda ya faru da shi har gawar ta fara rubuwa.

Olanrewaju ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa shine ya kashe Babalola saboda yin tsafi a yayin da ya ke amsa tambayoyin yan sanda.

A yayin zartar da hukunci, mai sharia Adedotun Onibokun ya samu wanda ake zargi da laifi.

Daga bisani ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A wani labarin, wata mata mai suna Alexandra Dougokenski ta kashe dan ta mai shekaru 11 ta hanyar sheke masa wuya saboda ta gaji da halinsa na buga wasar game a wayansa ta salula cikin dare.

A cewar Daily Mail, Yan sanda a kasar Brazil sun gurfanar da ita a kan zargin kashe dan ta mai suna Rafael a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli bayan ta amsa cewa ta aikata laifin.

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan Rafael ya rubuta wasu baitocin waka inda ya ke bayyana irin kaunar da soyayya da ya ke yi wa mahaifiyarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel