Covid-19: Wani mutum ya siya takunkumin fuska ta gwal kan kudi N1.5m (Hotuna)
Wani mutum ɗan ƙasar Indiya ya kashe kimanin Naira miliyan 1.5 don siyan takunkumin fuska da zai kare kansa daga coronavirus.
A cewar AFB, gwal ɗin da aka yi amfani da shi wurin ƙera takunkumin ya kai gram 60.
Ɗan kasuwan mai suna Shankar Kurhade mazaunin yammacin birnin Pune ya ce mutanen da suka ƙera takunkumin sun kwashe kimanin kwanaki takwas suna aikin.
"Takunkumin siriri ne kuma yana da ƙananan rami na shan iska ta zai ke taimaka min wurin numfashi," Shankar ya shaidawa AFP.
DUBA WANNAN: An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)
A duk lokacin da zai fita attajirin mai shekaru 49 ya kan ƙawata jikinsa da gwala-gwalai da nauyinsu ya kai kilogram ɗaya da suka haɗa da awarwaro, sarƙar wuya da zobe a yatsunsa na dama da hagu.
Kurhade wanda ya mallaki kamfanin ƙere-ƙere ya ce ya yanke shawarar ƙera takunkumin fuskar ne bayan ya ga labarin wani mutum a kafar watsa labarai da ke amfani da takunkumi na tagwulla.
"Mutane su kan yawan neman mu ɗauki hoton selfie," in ji shi.
"Na kan burge su idan sun ga na saka takunkumin gwal a kasuwanni."
Ƙasar Indiya ta wajabta wa mutanen ƙasar saka takunkumin fuska a wuraren taruwar mutane a yunƙurin ta na daƙile yaɗuwar mugunyar cutar.
Alƙalluma sun nuna cewa kimanin mutum 650,000 ne suka kamu da cutar a Indiya inda ta yi ajalin fiye da mutum 18,600.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Gwamnatin kasar China ta ce ta tabbatar da bullar wata cuta mai saurin yaduwa mai suna 'bubonic plague' wato annobar bubunic.
Hakan na zuwa ne watanni bayan bullar annobar COVID-19 da aka gano a birnin Wuhan a kasar ta China.
A cewar kafar watsa labarai na Xinhua, an samu mutum daya mai cutar a yankin Mongolia kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Hukumar Lafiya ta kasar ta ce an gano cutar a jikin wani makiyayi ne a ranar Lahadi amma baya cikin hatsari kuma ana masa magani a wani asibiti kamar yadda New York Times ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng