'Yan sandan da su ka kama Magu sun birkice gidansa a Abuja

'Yan sandan da su ka kama Magu sun birkice gidansa a Abuja

Wasu jami'an 'yan sanda da ke aiki da sashen binciken manyan laifuka (FCIID) sun birkice gidan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaba Buhari ya dakatar.

Wani babban jami'in dan sanda ya tabbatarwa da jaridar 'Punch' cewa an gudanar da bincike a gidan Magu da ke kan titin Abduljalil a unguwar Karu da ke wajen birnin tarayya, Abuja.

Babban jami'in ya bayyana cewa sun kwashe wasu muhimman takardu daga gidan Magu bayan sun shafe sa'o'i su na gudanar da bincike.

Jaridar Punch ta rawaito cewa 'yan sandan da su ka kama Magu ranar Litinin su ne su ka gudanar da bincike a gidansa ranar Talata.

"Da yammacin ranar Talata ne tawagar jami'an 'yan sanda ta dira gidan Magu da ke Karu.

"Nan ne gidan da Magu ya ke zaune kafin ya koma unguwar Maitama bayan an nada shi mukaddashin shugaban hukumar EFCC.

"Mun tafi da wasu muhimman kayayyaki da za su taimaka wajen cigaba da gudanar da bincike a kansa," a cewar babban dan sandan.

Kazalika, Punch ta wallafa cewa an cigaba da tsare Magu a rana ta biyu bayan ya shafe kusan sa'o'i biyar ya na amsa tambayoyi a gaban kwamitin bincike ranar Talata.

An kara mayar da shi wurin da aka tsare shi da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talata.

Majiyar Punch ta sanar da ita cewa rundunar 'yan sanda ta na gudanar da wani bincike na daban a kan Magu bayan binciken da kwamitin shugaban kasa ke gudanarwa a kansa.

'Yan sandan da su ka kama Magu sun birkice gidansa a Abuja
'Yan sanda a kofar gidan Magu
Asali: Facebook

A ranar Litinin ne Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin bincikensa da aka kafa a fadar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Badakala: An bankado wata makarantar FG da ake biyan mai shara albashin N32m

Bayan ya bar gaban kwamitin a ranar Litinin, jami'an rundunar 'yan sanda sun yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu, inda aka tsare shi har zuwa ranar Talata.

Lauyan Magu, Oluwatoyin Ojaomo, ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.

Ojaomo ya bayyana hakan ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels yayin da ya ke mayar da martani a kan gayyatar da wani kwamitin shugaban kasa ya yi wa Magu a yau, Litinin.

Lauyan ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama'a.

A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihun gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel