Magu ya tattara kayansa daga hedkwatar EFCC

Magu ya tattara kayansa daga hedkwatar EFCC

- Dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya fitar da wasu daga cikin kayayyakinsa da ke hedkwatar hukumar

- Hadiman Magu ne suka fitar wasu daga cikin kayayyakin nasa a yau Talata, 7 ga watan Yuli

- Hakan na zuwa ne yayinda fadar shugaban kasa ta kaddamar da cewa binciken Magu da ake yi ya tabbatar da cewar babu wanda ya fi karfin bincike a gwamnatin nan

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, ya fitar da wasu daga cikin kayayyakinsa da ke hedkwatar hukumar, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A cewar wasu majiyoyi na tsaro, shugaban na EFCC ya umurci hadimansa da su fitar da kayyayinsa daga ofis din a safiyar ranar Talata.

Ya bayar da umurnin ne yayinda yake a hanyarsa na zuwa fadar shugaban kasa don ci gaba da amsa tambayoyi a rana na biyu.

Majiyar ta bayyana cewa hadimansa sun zo hedkwatar EFCC a cikin motoci biyu don kwashe wasu daga cikin kayayyakin.

Magu ya tattara kayansa daga hedkwatar EFCC
Magu ya tattara kayansa daga hedkwatar EFCC Hoto: The Nation
Asali: UGC

An kuma tattaro cewar hadiman na iya dawowa a ranar Laraba domin kwashe abubuwan da suka rage a ofis din.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayinda fadar shugaban kasa ta kaddamar da cewa binciken Magu da ake yi ya tabbatar da cewar babu wanda ya fi karfin bincike a gwamnatin nan.

Wa majiya ta bayyana cewa binciken da ke gudana a kan Magu, ya kasance ne domin bashi damar amsa zarge-zargen da ake yi a kansa.

KU KARANTA KUMA: Mai Mala Buni ya bayyana dalilin sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo da SSG

Majiyar ta jadadda cewar binciken Shugaban na EFCC ya kasance domin tabbatar da jajircewar gwamnatin Buhari wajen adalci da gaskiya.

Ta kuma ce dole ce ta sa kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Ayo Salami saboda tangardar da aka samu wajen yaki da rashawar.

A cewar majiyar: “kwamitin da ke binciken zarge-zargen da ake yi a kan mukaddashin shugaban na EFCC ya kwashe tsawon wasu makonni yana zama.

“A yarjejeniyar da ke tattarin da tsarin gaskiya da adalci, akwai bukatar ba mukaddashin shugaban hukumar damar amsa tuhume-tuhume da ake masa, wadanda suka kasance masu girman gaske.

“A karkshin gwamnatin Muhammadu Buhari, babu wanda ya fi karfin bincike. Na maimaita: babu wani."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng