Korona: Dubai ta sanar da bude kasar ga ma su yawon bude ido
A ranar Talata ne kasar Dubai ta sanar da bude iyakokinta ga bakin haure ma su yawon bude ido bayan shafe kusan watanni hudu a karkashi dokar kulle.
Gwamnatin kasar ta ce za a gudanar da gwajin cutar korona a kan dukkan bakon da ya shiga kasar.
Bude iyakokin kasar ga ma su yawon bude ido na zuwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda suka kamu da cutar korona ya hau sama zuwa mutum 52,068 da suka hada da mutane 324 da suka mutu.
Yawancin bakin haure 'yan ci rani na zaune ne a cakude cikin takura a muhallinsu lamarin da ya haifar da yawaitar ma su cutar korona a cikinsu.
Ana bukatar bakin da za su shiga kasar su gabatar da takardar shaidar yi mu su gwajin cutar korona a cikin kwanaki hudu kafin barin kasarsu.
Gwamnatin kasar ta ce za ta gudanar da gwajin korona nan take a kan duk wani bako da bashi da takardar shaidar yi ma sa gwajin korona daga kasarsa, sannan tilas ya killace kansa har sai sakamakon gwajinsa ya fito.
Kasar Dubai ta na samun makudan kudade daga bakin haure da ke ziyartar kasar domin yawon bude ido.
DUBA WANNAN: Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son bayan ganin maigidansa
A shekarar da ta gabata, 2019, 'yan yawon bude ido mutum miliyan 16.7 sun ziyarci kasar Dubai kafin annobar korona ta tsayar da al'amura a 2020, shekarar da kasar Dubai ke saka ran karbar bakuncin ma su yawon bude ido mutum miliyan 20.
"A shirye mu ke mu fara karbar bakin haure 'yan yawaon bude ido, mun dauki dukkan matakan da suka dace," a cewar Talal Al-Shanqiti na sashen harkokin kasashen ketare na kasar Dubai a cikin wani sako da ya wallafa ranar Lahadi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng