Boko Haram ta tabbatar da ƙawancenta da ƴan bindigan Niger cikin sabon bidiyo
Kungiyar Jama’atu Ahlussunnah Lidda’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram bangaren Abubakar Shekau sun tabbatar da alakarsu da 'yan bindigan da ke jihar Niger a yankin Arewa maso yammacin Najeriya cikin wani sabon bidiyo da suka fitar.
A cikin bidiyon mai tsawon minti shida dakika biyar an gano mayakan kungiyar taadancin suna magana da harshen Hausa, Turanci da Kanuri kamar yadda HumAngle ta ruwaito.
Mayakin da ya yi magana da farko sanye da takunkumi a fuskarsa ya yi magana ne cikin harshen hausa kamar haka;
"Gaisuwa ta musamman daga dan uwanku mai jihadi da ke Tafkin Chadi. Gaisuwa ga shugaban mu Abu Muhammad Ibn Muhammad Abubakar Asshakawy.
"Wannan sakon tawa zuwa ga masu jihadi ne a ko ina, musamman wadanda ke kusa da mu. Muna muku gaisuwa irin ta addinin musulunci.
DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)
"Sakona na biyu kuma zuwa ga dukkan wadanda ba su yi imani bane a dukkan sassan duniya. Ku tuba, kuna da sauran lokaci. Idan kuma ba ku tuba ba, ku jira ku ga abinda zai faru da ku nan ba da dadewa ba," in ji shi.
Wasu kuma sunyi magana da harsunan turanci da Kanuri inda suka maimaita sako mai kama da na farkon.
Wanda ya yi magana da turanci ya ce, "Sako na ga kafurai. Ya ku kafurai, kuna da daman ku tuba ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala kafin ya hukunta ku da hannunsa.
"Cikin kankanin lokaci, za ku ga abinda zai faru a kasuwannin ku. Za kuma ku ga abinda zai faru a ofisoshin ku.
"Nan ba da dadewa ba za ku ga abinda zai faru a gidajenku. Duk inda ku ke, za ku ga abinda zai faru da ku."
Wani dan ta'adda ya yi alkawarin gano duk dan leken asirin da Rundunar Sojin Najeriya ta tura cikinsu don ya rika kawo mata rahoto.
A baya, HumAngle ta ruwaito cewa kungiyoyin ta'adda na yankin Arewa maso yamma suna shirin hadin gwiwa tare da sauran kungiyoyin ta'adda a Arewa maso tsakiya da Arewa maso yamma.
A bidiyon da aka fitar yau, Talata, wani mayaki da aka nuna ya ce shi dan asalin jihar Niger ne kuma yana aika gaisuwa ga yan uwansa da ke Sambisa, Tafkin Chadi da Zamfara.
Ya ce, "Muna aika gaisuwa da yan uwanmu da ke Sambisa, Tafkin Chadi da Zamfara."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng