Zaben gwamna: PDP ta karbi sabbin 'yan adawa 106 a jihar Edo
Biyo bayan sauyin shekar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, daga jam'iyyar APC zuwa PDP, mambobin jam'iyyar ADP 106 sun sauya sheka daga jam'iyyar ADP zuwa PDP.
Mambobin jam'iyyar ta ADP da suka sauya sheka zuwa PDP sun fito ne daga kananan hukumomin Ovia ta kudu maso yamma da Obia ta arewa maso gabas.
Sauyin shekar mambobin na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage watanni biyu kacal a gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Edo.
Za a fafata a zaben ne a tsakanin gwamnan mai ci, Godwin Obaseki, da babban abokin hamayyarsa; Fasto Osagie Ize-Iyamu, dan takarar jam'iyyar APC kuma tsohon dan takarar jam'iyyar PDP.
Da ya ke magana amadadin sauran ma su sauya shekar a yau, Talata, a birnin Benin, sakataren tsare - tsaren jam'iyyar ADP, Oshodin Izedomwen, ya ce sun sauya sheka ne bisa amannar cewa PDP ce za ta lashe zaben da za ayi ranar 19 ga watan Satumba.
Izedomwen ya ce ya na daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP amma halayyar wasu bakin mambobin jam'iyyar suka tilasta shi ficewa.
Ya bayyana shi da sauran mutanen da suka sauya sheka sun zabi dawowa jam'iyyar PDP ne saboda balagurbin cikinta sun fita.
"Bukata ce take sanya a shiga siyasa, bukata ce take rike da dimokradiyya gaba dayanta," a cewarsa.
DUBA WANNAN: Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son ganin bayan maigidansa
A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa ranar Litinin, Mista Idefayo Abegunde, sakataren gwamnatin jihar Ondo, ya yi murabus daga mukaminsa a yau, Litinin, 06 ga watan Yuli, kamar yadda kafafen watsa labarai da dama suka wallafa.
Abegunde, wanda aka fi sani da 'Abena', ya mika takardarsa ta barin aiki da safiyar ranar Litinin.
Sai dai, Abegunde ya yi gum da bakinsa a kan dalilin da yasa ya zabi yin murabus a daidai lokacin da zabe ke kara matsowa kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ke zaman jinyar cutar korona.
Da yake magana da jaridar The Nation ta wayar tarho, Abegunde ya tabbatar da cewa ya mika takardarsa ta barin aiki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng