Tsohon shugaban hukumar DSS ya bai wa Magu shawara
Tsohon mataimakin darakta a hukumar tsaro ta farin kaya, Dennis Amachree, ya ce da shine yake fuskantar zargin rashawa kamar yadda dakataccen mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu ke fuskanta, babu shakka murabus zai yi.
Amachree ya sanar da hakan ne a gidan talabijin na Channel a wani shirin su na ranar Talata.
Ya ce akwai matukar wahala Magu ya tafi haka saboda yawan zargin da ke gaban kwamitin fadar shugaban kasar.
Tsohon jami'in DSS ya ce, koda bayan kammala bincike an gano cewa Magu bashi da wani laifi, abinda ya fi mishi shine yin murabus.
Amachree ya ce, ya sha matukar mamakin yadda shugaban kasar ya aminta da shi duk da majalisar dattawa sun ki tabbatar da shi har sau biyu bayan mika sunansa a gabansu.
Ya ce, yadda kwamitin binciken ke zama a fadar shugaban kasa ke nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yasa a yi binciken.
Amachree ya ce, "Idan da ni ne Magu na je gaban kwamitin binciken, kuma suka wanke ni cewa bani da wani laifi, ina fitowa zan yi murabus."
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC amsa tambayoyi
A ranar Litinin ne aka gayyaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar.
An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a 'Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa. An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar.
Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami'in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar.
Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci. Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.
A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar.
Wata majiya ta ce: "Magu da Jacob a halin yanzu suna wani ofishin da ke fadar shugaban kasar.
"Ba a kama shi ba, kuma babu wata hukumar tsaro da ta damke shi. Muna sauraron ci gaban da zai faru a gaba."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng