Dole ne Magu ya sauka don bada damar bincike mai inganci - PDP

Dole ne Magu ya sauka don bada damar bincike mai inganci - PDP

- Jam'iyyar PDP ta bukaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu da ya sauka daga kujerarsa bayan gayyatar da DSS ta yi masa

- PDP ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna ingancin ikirarin yaki da rashawa da yake yi ta hanyar bari a bincike Magu yadda ya dace

- Ta ce Magu ya rasa nagartar da za a barshi ya ci gaba da shugabantar cibiyar yaki da rashawa ta kasar nan

Jam'iyyar PDP ta bukaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu da ya sauka daga kujerarsa bayan gayyatar da ya samu daga hukumar jami'an tsaro ta farin kaya a ranar Litinin.

Magu wanda aka gayyata don amsa tambayoyi a gaban kwamitin gwamnatin tarayya, ana zarginsa da rashawa.

Gayyatar ta janyo cece-kuce wacce ta sa aka dinga ruwaito cewa kama shugaban hukumar EFCC din aka yi.

Dole ne Magu ya sauka don bada damar bincike mai inganci - PDP
Dole ne Magu ya sauka don bada damar bincike mai inganci - PDP Hoto: Politics Nigeria
Asali: UGC

A yayin martani game da hakan, PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna ingancin ikirarin yaki da rashawa da yake yi ta hanyar bari a bincike Magu yadda ya dace, Channels TV ta ruwaito.

PDP ta ce 'yan Najeriya tuni suka san cewa an kira Magu don amsa tambayoyi kuma ya samu rakiyar lauyansa, hakan na nuna cewa gayyatar ba kowacce iri bace.

Jam'iyyar ta ce wannan lamari na mukaddashin shugaban EFCC na nuna yadda ake kokarin rufa-rufa game da hukumar, kuma cewa hakan ya janyo hankalin jama'a a kan zargin nagartar ayyukan EFCC.

Takardar ta kara da cewa, "A watan da ya gabata ne, Antoni janar Abubakar Malami ya saki wata takarda wacce ta nuna zargin waskar da wasu kudade tare da damfarar wasu kadarori da aka kwato ta wurin hukumar.

"Jam'iyyarmu, 'yan Najeriya da dukkan duniya na natse suna kallon wannan ci gaban kuma ana sa ran shugaba Buhari zai samu kwarin guiwar bada damar yin binciken tare da bayyana wa jama'a abinda aka gano.

"A yanzu da Magu yake gaban bincike, gwamnatin tarayya ta tsare nagartar ofishin sa ta hanyar umartarsa da ya sauka daga kujerarsa don gujewa lalata dukkan shaidu ko hana bincike mai nagarta."

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja

Jam'iyyar PDP ta sanar da cewa, Magu ya rasa nagartar da za a barshi ya ci gaba da shugabantar cibiyar yaki da rashawa ta kasar nan.

PDP ta shawarci Magu da ya yi murabus har sai an tabbatar da gaskiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng