'Yan bindiga sun kashe manoma 15 a Katsina

'Yan bindiga sun kashe manoma 15 a Katsina

Kamar yadda rahoto daga kauyen 'yar Gamji na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ya bayyana, wasu 'yan bindiga 200 dauke da miyagun makamai sun kai hari tare da kashe mutane sama da 15.

'Yan bindigar da suka tsinkayi kauyen a kan babura, sun halaka manoman da suka samu a gona.

'Yan bindigar sun isa kauyen wurin karfe 10 na safe kuma sun yi ruwan wuta na a kalla sa'a daya, mazauna yankin suka sanar da Daily Trust.

"Bayan 'yan bindigar sun gama ruwan wuta, mun je inda muka dauke gawawwakin. Mun kirga gawawwaki 15," daya daga cikin mazauna kauyen ya sanar duk da ya bukaci a sakaya sunansa.

Ya sanar da cewa a yau za a birne mamatan.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda 'yan bindigar suka isa kauyen 'Yar Gamji wanda ke kan titin Katsina zuwa Dutsinma zuwa Kankara zuwa Funtua. Yana da nisan kilomita a kalla 30 daga cikin garin Katsina.

'Yan bindiga sun kashe manoma 15 a Katsina
'Yan bindiga sun kashe manoma 15 a Katsina. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: PSC ta kori manyan 'yan sanda 10 daga aiki

A nan ne babbar hedkwatar 'yan sanda take, bataliyar dakarun soji da kuma filin saukar jirgin da ke kawo kayan aikin yaki da ta'addancin da ya addabi yankin arewa maso yamma.

A titi kuwa, 'yan sanda ko sojoji za su iya daukar mintuna 30 zuwa kauyen daga Katsina don bibiyar 'yan bindigar.

A jirgin sama kuwa, za a iya daukar mintuna 10 don isa wurin da 'yan bindigar suka kai hari. Wuri ne wanda ya kusa zama hamada don babu daji.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da kashe-kashen.

Ya ce ruwan sama ne yasa manoma da yawa suka hanzarta zuwa gonakinsu yayin da 'yan bindigar suka yi amfani da wannan damar wurin kai musu hari.

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram masu tarin yawa da kayan aikinsu a harin da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai Mina, kusa da Gulumba da kuna yankin Gana-Kumshe a yankin arewacin jihar Borno.

Wannan ragargazar da dakarun suka yi wa mayakan ta'addancin ta hargitsa su tare da halaka sabbin shugabanninsu. Hakan ya faru ne a ranar 3 ga watan Yulin 2020.

Bayan rahotannin sirrin da rundunar sojin ta samu na wurin da mayakan suka koma da kuma inda kayan aikinsu suke, ta jiragen yaki dakarun suka tabbatar da ingancin zancen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel