Yadda Shehu Sani ya karba N4m a hannuna zai bai wa alkalai - Shaida

Yadda Shehu Sani ya karba N4m a hannuna zai bai wa alkalai - Shaida

A ranar Litinin, shaidar masu gurfanarwa, Alhaji Sani Dauda, ya sanar da babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa, Sanata Shehu Sani ya bukacesa da ya bai wa alkalai hudu miliyan daddaya don su taimaka a kan shari'arsa.

An gurfanar da tsohon sanatan ne a kan laifuka biyu da suka hada da cin hanci tare da babbar damfara wacce hukumar yaki da rashawa ke bincikarsa.

A lokacin da aka kira shari'ar, alkalin ya bada umarnin dakatawa na mintoci 15 don samun tafintan shaidu biyun da ke kotu.

Tafintan Alhaji Sani Dauda ya sanar da kotun cewa, an kama shi tare da dukkan iyalansa amma an sakesu a ranar 15 ga watan Disamnan 2019.

Kamar yadda Dauda yace, bayan sakinsa, Sani ya je masa jaje inda yace yana son ganinsa.

A yayin da muka hadu a gidana da ke Maitama, ya sanar dani cewa akwai bukatar in bai wa alkalai kudi a kan shari'ata.

"Ya ce min ya samu tattaunawa da alkalin alkalan Najeriya a kan shari'ar.

"Ya ce in yi magana da alkalin alkalan amma na sanar da shi cewa zan so ganin alkalin alkalan. A nan yace babban alkalin baya son jama'a na kai masa ziyara gidansa tunda jami'an tsaro da suka hada har da na farin kaya na kallon wadanda ke shige da fice.

"Ya yi kira sannan ya bani wani mutum, mutumin yace Sani ya yi masa magana a kan shari'ata kuma ya yi wa alkalai hudu magana.

"Sani ya ce in bai wa kowanne alkali miliyan daya amma na sanar da shi cewa tunda wannan kaddarar ta fada min, bani da kudi.

"Ya kara da sanar dani cewa Abubakar na da matsala a gaban EFCC kuma suna bukatar miliyan daya, hakan ne yasa zan bada miliyan biyar. Na ce bani da kudi a ranar amma ya dawo gobe.

Yadda Shehu Sani ya karba N4m a hannuna zai bai wa alkalai - Shaida
Yadda Shehu Sani ya karba N4m a hannuna zai bai wa alkalai - Shaida. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: PSC ta kori manyan 'yan sanda 10 daga aiki

"Daga nan na kira dan canji, Abubakar ya kawo min kudin," yace.

A yayin da mai bada shaidar ke kokarin bayanin yadda ya samu canjin dalolin zuwa Naira, alkalin yace bai gamsu da tafintan ba.

A wani lokacin, bai gamsu da yadda ake bayyana abinda shaidar ke cewa ba ballantana wurin da ake lissafo kudin.

Alkalin ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Yuli tare da bada umarnin a samo wani tafinta.

Tun a farko, Bala Ismail,wani shaidar masu gurfanarwa wanda ma'aikacin Dauda ne, ya sanar da kotun cewa tsohon sanatan ya ziyarci ubangidansa sau biyar kafin a fara kullen dakile yaduwar korona.

Ya ce dai bai san abinda suka tattauna ba, kuma bai san abinda Sani ya karba ba a ambulan mai ruwan kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng