Yadda ƴar sanda ta bindige mijinta don bai amsa wayarta ba

Yadda ƴar sanda ta bindige mijinta don bai amsa wayarta ba

Wata ƴar sanda a ƙasar Kenya ta harbi mijinta da bindiga AK-47 a unguwar Dago da ke Nyalenda, Kisumu saboda bai daga ƙirar wayan da ta masa ba.

Matar da aka ce sunan ta APC Maureen yanzu ta tsere ba a san inda ta shiga ba.

Ƴar sandan da ke zaune a Kisumu da ke Gabashin ƙasar ta harbi mijinta ne saboda ya bawa ƴar aikinsu kuɗi Ksh50 don sayan abincin rana ba tare da tambayar ta ba kuma baya ɗaga wayan ta.

Yadda ƴar sanda ta bindige mijinta don bai amsa wayarta ba
Yadda ƴar sanda ta bindige mijinta don bai amsa wayarta ba. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Rahoton ƴan sanda ya tabbatar da cewa mijin ƴar sandar da ke asibitin Kisumu ya samu rauni a gefen kansa na dama a saman kunensa.

Rahoton ya ƙara da cewa ta harbe shi ne a yayin da ya ke kallon talabijin a gida.

"Ta tsaya a ƙofa riƙe da bindiga AK-47. Ta faɗa masa cewa za ta kashe shi sannan ta gyara bindigar ta harbe shi sau biyu ta yi masa rauni a kansa daidai saman kunensa.

"Daga nan kuma ta tsere bayan ta mayarwa abokiyar aikinta, APC Nancy bindigar a ofis."

KU KARANTA A fuska ya ke jefa min kororon roba idan ya dawo lalata da ƴan mata - Mata ta fadawa kotu

K2TV ta ruwaito cewa an garzaya da mijin matar zuwa asibitin Kisumu inda akayi masa magani kuma aka sallame shi.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar ƴan Sandan Jihar Ebonyi a ranar Juma'a ta gurfanar da wani Obiemezie Chiekezie gaban kotun gargajiya da ke zamanta a Abakaliki kan sace wayar wata alƙaliya.

Alƙaliyar, Mrs Ezeugo Esther ta fita motsa jiki da safe ne misalin ƙarfe 5.30 na asuba a Nna Street inda wanda ake zargin ya fizge wayan daga hannunta ya tsere.

An yi ƙoƙarin bin sahunsa a ranar amma ba ayi nasara ba har sai ranar Laraba da ƴan sanda suka gano shi.

An gurfanar da Chiekezie a ranar Juma'a a kan tuhumarsa da yin sata.

Ba a shigar da buƙatar neman beli ba duba da cewa babu lauya mai kare wanda ake zargin a kotun.

Amma a yayin yanke hukunci, shugaban Kotun, Mrs Nnenna Onuoha ta bayar da belinsa kan kudi Naira miliyan 1 da mutum ɗaya da zai tsaya masa.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel