Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son ganin maigidansa

Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son ganin maigidansa

Oluwatoyin Ojaomo, lauyan mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.

Ojaomo ya bayyana hakan ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels yayin da ya ke mayar da martani a kan gayyatar da wani kwamitin shugaban kasa ya yi wa Magu a yau, Litinin.

Lauyan ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama'a.

A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihu gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace.

"Idan kana yaki da cin hanci, ka sani cewa cin hanci zai yakeka, cin hanci ya yi karfi sosai, ma su cin hanci sun yi karfi, sun fi annobar korona karfi.

"Yanzu ku duba abinda yake faruwa, sakamakon a yabawa Magu, manyan mutanen da suka yi karfi saboda cin hanci suna kokarin bata ma sa suna ta hanyar amfani da kafafen yada labaran da su ka mallaka," a cewar Ojaomo.

Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son ganin maigidansa
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Lauya ya kara da cewa; ''EFCC ta na cigaba da kwace kadarori daga hannun mabarnata a kowacce rana, a saboda haka ba abin mamaki bane don an samu banbanci a tsakanin kudin da aka karba da wanda aka sanar a baya''.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ta ce ba ta kama mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ba.

DUBA WANNAN: Ondo 2020: Mataimakin gwamna ya sauya sheka, SSG ya yi murabus ana daf da zabe

A cikin wata sanarwa da jami'an hulda da jama'a, Peter Afunanya, DSS ta ce babu gaskiya a cikin labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa ta kama Magu.

"Hukumar DSS ta na son sanar da jama'a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFFC, ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.

"DSS ta fitar da wannan sanarwa ne a yau, Litinin, 6 ga watan Yuli, bayan yawan tuntubarta a kan zargin kama Magu," a cewar sanarwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng