COVID-19 ta kwantar da Shugaban NMA Dr. Bulus Peter a jihar Nasarawa

COVID-19 ta kwantar da Shugaban NMA Dr. Bulus Peter a jihar Nasarawa

Shugaban kungiyar NMA ta likitocin jihar Nasarawa, Dr. Bulus Umaru Peter ya kamu da kwayar cutar COVID-19.

Jaridar The Nation ta ce Bulus Umaru Peter ya fara jin wasu daga cikin alamomin wannan cuta a jikinsa, wanda hakan ya sa ya je ya yi gwaji.

Kwanaki hudu bayan an dauki majinar wannan babban likita, sai sakamako ya nuna cewa ya na dauke da Coronavirus.

Wani na-kusa da likitan ya shaidawa jaridar cewa Bulus Umaru Peter ya kamu da cutar ne a wajen wani aiki da ya yi tun kwanaki.

Dr. Bulus Umaru Peter ya na cikin masu aikin kula da wadanda su ka kamu da COVID-19 a garin Lafia da ke cikin jihar Nasarawa.

Rahotanni ya bayyana mana cewa rashin gado ya sa dole aka kwantar da shugaban na NMA a gidansa domin ya yi jinya.

KU KARANTA: Sharararrun mutane da COVID-19 ta kashe a ranar Lahadi

COVID-19 ta kwantar da Shugaban NMA Dr. Bulus Peter a jihar Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa
Asali: UGC

Babu isassun gadon da za a ajiye masu jinyar Coronavirus a dakin killace masu cutar da ke Lafia, don haka Likitan ya killace kansa a gida.

Da aka yi magana da Dr. Peter, sai ya ce: “Ta tabbata daga sakamakon gwajin NCDC cewa na kamu da COVID-19.”

Malamin asibitin da ke kwance yanzu a gado ya kara da cewa: “Amma yanzu ina samun lafiya.”

Zuwa ranar 3 ga watan Yuli, malaman kiwon lafiya masu dauke da cutar COVID-19 a jihar Nasarawa sun kai 65.

Daga cikin wadannan ma’aikatan asibiti akwai 51 da ke aiki da asibitocin gwamnati, 14 su na aiki da asibitocin kasuwa.

COVID-19 ta shiga kananan hukumomin jihar Nasarawa irinsu Karu, Keffi, Nasarawa Eggon da kuma Lafia inda shugaban na NMA ya ke kwance.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel