Rundunar 'Hadarin Daji' ta yi wa 'yan daban daji ruwan wuta a Zamfara da Katsina

Rundunar 'Hadarin Daji' ta yi wa 'yan daban daji ruwan wuta a Zamfara da Katsina

A fafutikar da dakarun sojin Najeriya ke yi domin kawo karshen ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma, sun samu nasarar yi wa masu tayar da kayar baya luguden wuta a jihohin Katsina da Zamfara.

A ranar 3 ga watan Yuli, rundunar sojin kasan Najeriya ta samu nasarar kai wani hari kan 'yan daban daji a sansaninsu na kauyen Sanu da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Rundunar musamman ta Operation HADARIN DAJI mai yaki da masu tayar da kayar baya a Arewa maso Yamma, ta samu nasarar yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta na bazata.

An cimma wannan gagarumar nasara ta hanyar kai hare-hare babu sassauci tun bayan kaddamar da sabon aikin dakaru da aka yi wa lakabi da "Operation ACCORD".

Operation ACCORD wani sabon shiri ne da dakarun sojin suka fara gudanar da shi a baya bayan nan domin kara kaimi da zage dantse wajen kawo karshen 'yan ta'adda a yankin.

Legit.ng ta samu rahoton hakan ne cikin wata sanarwa da jami'in gudanarwa na rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche ya fitar a wani sako da ya wallafa kan shafin Twitter a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Rundunar 'Hadarin Daji' ta yi wa 'yan daban daji ruwan wuta a Zamfara da Katsina
Rundunar 'Hadarin Daji' ta yi wa 'yan daban daji ruwan wuta a Zamfara da Katsina
Asali: Twitter

A yayin amfani da dabaru da kwarewa, sojoji sun mamaye sansanin 'yan ta'addan, inda suka yi musu kawanya. Wasunsu sun samu nasarar tserewa da raunuka na harbin bindiga.

Haka zalika, a yayin tsananta kai simame, dakarun sojin sun yi kicibus da 'yan daban daji a kauyen Bawan Daji, inda nan take suka sheke guda daga cikinsu yayin da da dama suka tsira da raunuka na harbin harsashi.

KARANTA KUMA: Waiwaye: Gwamnatin Yar’Adua ta gaza - Buhari, Atiku da sauransu

A yayin haka dai, dakarun sun kai hari wani sansanin 'yan ta'adda a yankin Gidan Zamfarawa, tazarar kilomita 10 da kauyen Mashanyin Zaki.

Bayan da 'yan daban dajin suka hangi rundunar dakarun, sun arta a guje, lamarin da ya sanya suka zub da makamai da dama ciki har da bindigu kirar AK-47 da kuma baburan hawa.

A ranar Lahadi, 5 ga watan Yuli, dakarun sojin sun kuma fantsama sansanin 'yan ta'adda da ke kauyen Salihawa na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, inda suka samu nasarar kashe daya daga cikinsu.

Sojojin a ranar 4 ga watan Yuli, sun kuma kama wanda ake zargi yana yi wa 'yan ta'addan jigiliar kayayyakin bukata, Mohammed Illela a kauyen Illela, bayan samun wasu bayanan sirri.

An kama wanda ake zargin yayin da yake kokarin isarwa da 'yan ta'addan jarkunan man fetur 13 da aka boye su cikin wata mota kirar Volkswagen mai launin toka.

A wannan rana dai ta 5 ga watan Yuli, dakaru sun samu nasarar tsinto miyagun makamai yayin wani sintiri da tsefe kauyen Bawar Daji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel