Yanzu-yanzu: DSS ta hana 'yan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a Aso Villa
- Jami'an hukumar tsaro na farin kaya, sun hana manema labarai shiga dakin taron da shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ke amsa tambayoyi
- A yau Litinin ne dai labarin damke Magu ya bayyana inda aka zargin hukumar DSS da aikata kamun nasa
- Manema labaran fadar shugaban kasa sun gangara dakin taron da shugaban EFCC yake don tabbatar da wannan ci gaban amma jami'an DSS suka fatattake shi
A ranar Litinin, jami'an hukumar tsaro na farin kaya, sun hana manema labarai shiga dakin taron da shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ke amsa tambayoyi.
A ranar Litinin ne labarin damke Magu ya fara yaduwa wanda ake zargin hukumar tsaro ta farin kaya tayi.
Amma kuma, manema labaran gidan gwamnati sun gangara dakin taron da shugaban EFCC yake don tabbatar da wannan ci gaban.
Sai dai kuma jami'an DSS wadanda ke dankare a farfajiyar domin taron sun umarci manema labarai da su bar wurin, jaridar The Nation ta ruwaito.
"Sun ce ku hakura da amfani da wannan wurin na yau," wani jami'in ya sanar da manema labarai cike da tausasa murya.
Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa an gayyaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar.
An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a 'Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa.
An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar.
Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami'in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar. Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci.
Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.
A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng