'Babu hannunmu': DSS ta yi karin haske a kan kama Ibrahim Magu
Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ta ce ba ta kama mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ba.
A cikin wata sanarwa da jami'an hulda da jama'a, Peter Afunanya, DSS ta ce babu gaskiya a cikin labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa ta kama Magu.
"Hukumar DSS ta na son sanar da jama'a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFFC, ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.
"DSS ta fitar da wannan sanarwa ne a yau, Litinin, 6 ga watan Yuli, bayan yawan tuntubarta a kan zargin kama Magu," a cewar sanarwar.
Duk da cewa hukumar DSS ta musanta rahoton cewa ta damke mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, an tsare shi a ofishin yan sanda.
An dakatar da dogaransa kafin a iya tafiya da shi.
Jaridar The Nation ta samu labarin cewa bayan zaman tambayoyin da akayi masa, an shigar da Magu wata mota fara kirar Hilux mai lamba 37ID.
Amma Magu ya ce sam ba zai shiga cikin ofishin ba, sai dai ya zauna a bayan motar.
Daga baya 'yan sandan suka shawo kansa ya shiga cikin motar. Daga karshe dai aka garzaya dashi ofishin binciken hukumar yan sanda sashen FCID a cikin motarsa.
DUBA WANNAN: Sun fi annobar korona karfi: Lauyan Magu ya yi magana a kan ma su son ganin bayan maigidansa
Wata Majiya tace: "Sakamakon binciken dake gudana yanzu, ya zama wajibi a garkame Magu a FCID.
''Bamu son ya koma ofishinsa yayinda ake bincikensa, saboda akwai yiwuwan a cigaba da yi masa tambayoyinsa da kwamitin Ayo Salami." An samu labari daren jiya cewa da yiwuwan a dakatad da Magu daga Ofis.
"Hana shi komawa ofishinsa alama ce dake nuna cewa za'a dakatar da shi."
"A bayyane take karara cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirin neman sabon wanda zai maye gurbinsa," a cewar majiyar.
Daga cikin tuhume - tuhume da ake yi wa Magu akwai; Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati, Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn.
Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya, rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya, bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda a hakan ya kai ga rikicin da ake yi a kotu yanzu haka da sauransu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng