Saudiyya ta haramtawa Mahajjata sanya hannu jikin Ka'aba a aikin Hajjin bana

Saudiyya ta haramtawa Mahajjata sanya hannu jikin Ka'aba a aikin Hajjin bana

Hukumomi masu kula da masallatan alfarma biyu a kasar Saudiya, sun sake sabunta wallafar ka'idodin da suka shata wanda za a kiyaye yayin gudanar da aikin Hajji a bana.

Makasudin wannan ka'aidodi kamar yadda mahukunta suka shar'anta, shi ne bai wa mahajja kariya daga cutar korona tare da dakile yaduwar cutar yayin sauke farali.

Jigo cikin sabbin ka'idodin da aka shar'anta, shi ne haramtawa Mahajjata kusantar Ka'aba ballantana har ta kai ga shafar wani sashen na jikinta ko kuma ɗamfara kirji da damatsan hannu kamar yadda aka saba.

Da wannan ne hukumomin suke shaidawa maniyyatan bana cewa, babu maganar shafar Dutsen Hajaral Aswad, wanda ya ke manne a kusurwar da ake fara daukan haramar dawafi.

Kamar dai yadda addinin Islama ya tanada, ana shafar Dutsen ne yayin da za a fara kowane nau'i na dawafi sannan a sumbaci hannu daka tabo dutsen da shi.

Aikin Hajji
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Aikin Hajji Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Asali: UGC

Sai dai kuma shafar dutsenda hannu bai zama wajibi ba, ana iya ishara izuwa gare shi sannan a tsunduma cikin dawafi.

Haka zakila, mahukuntan sun bukaci mahajjatan bana su rika bayar da tazara a tsakaninsu da juna ta tsawon mita daya da rabi yayin ibadu tare da tabbatar da sun sanya takunkumin rufe fuska.

Sakamakon yadda annobar korona ta dagula al'amura tare da hana ruwa gudu a fadin duniya, gwamnatin Saudiya ta takaice adadin mutanen da za a bai wa damar sauke farali a bana.

KARANTA KUMA: An kashe mutum uku, an sace shugaban jam'iyyar APC a Katsina

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Saudiyya ta fidda wasu sharruda da dukkan masu niyyar zuwa sauke farali a kasa mai tsarki a bana za su kiyaye.

Mahukunta a kasar ta Saudiyya a baya sun bayyana cewa mazauna kasar ta Saudiyya ne kawai za a bawa daman yin aikin hajjin a bana saboda annobar coronavirus.

A yayin taron manema labarai a ranar Talata, Ministan Lafiya na Saudiyya, Tawfiq Al-Rabiah ya ce za a bawa wadanda shekarunsu bai haura 65 ba da kuma masu cikakkiyar lafiya damar zuwa sauke faralin.

Ya kara da cewa za kuma a yi wa maniyyatan gwajin cutar korona kafin a bari su shiga kasa mai tsarkin kuma za su kwashe kwanaki 14 a killace a masaukinsu gabani da bayan kammala aikin hajjin.

A watan jiya ne ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta shata wasu sharuda guda takwas da suka shafi aikin hajjin na bana.

Jerin sharudan sun hadar da:

1. Wadanda shekarunsu ya haura 65 ba za su yi aikin Hajji ba

2. Mutane masu cututtuka kamar ciwon sukari, hawan jini da sauransu babu su a lissafin aikin hajjin na bana

3. Za a yi wa duk maniyyata gwajin cutar korona kafin a fara aikin Hajjin

4. Za a tabbatar da kiyaye dokar bayar da tazara yayin aikin Hajji

5. Za a rika duba lafiyar mahajjatan a kai- a kai.

6. Za a killace mahajjata na kwanaki 14 bayan kammala aikin Hajji.

7. Za a rika gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-kadan saboda tabbatar da dokar bayar da tazara.

8. Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura dubu 10 ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel