Ondo 2020: Mataimakin gwamna ya sauya sheka, SSG ya yi murabus ana daf da zabe

Ondo 2020: Mataimakin gwamna ya sauya sheka, SSG ya yi murabus ana daf da zabe

Mista Idefayo Abegunde, sakataren gwamnatin jihar Ondo, ya yi murabus daga mukaminsa a yau, Litinin, 06 ga waan Yuli, kamar yadda kafafen watsa labarai da dama suka wallafa.

Abegunde, wanda aka fi sani da 'Abena', ya mika takardarsa ta barin aiki da safiyar ranar Litinin.

Sai dai, Abegunde ya yi gum da bakinsa a kan dalilin da yasa ya zabi yin murabus a daidai lokacin da zabe ke kara matsowa kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ke zaman jinyar cutar korona.

Da yake magana da jaridar The Nation ta wayar tarho, Abegunde ya tabbatar da cewa ya mika takarsa ta barin aiki.

"Na bar gwamnatin Akeredolu, na mika takardar barin aiki kuma ta fara aiki daga yau (Litinin)," a cewarsa.

Abegunde ya ce zai bayyana dalilan da suka sa ya yanke shawarar yin murabus yayin taron da zai yi da manema labarai zuwa anjima.

Wata majiya ta bayyana cewa Abegunde ya bar gwamnatin Akeredolu ne saboda yana son tsayawa takarar mataimakin gwamna ga daya daga cikin 'yan takarar jam'iyyar APC, Segun Abraham.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Ondo a cikin watan Oktoba.

A ranar 21 ga watan Yuni ne mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Agboola Ajayi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ondo 2020: Mataimakin gwamna ya sauya sheka, SSG ya yi murabus ana daf da zabe
Mista Idefayo Abegunde
Asali: Twitter

Agboola ya sanar da barinsa jam'iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, jaridar Leadership ta ruwaito.

Agboola wanda ya sanya hannu a takardar fitarsa daga jam’iyya APC mai mulki a Ward 2 da ke Apoi a karamar hukumar Ese-Odo da ke jihar Ondo, sannan ya gaggauta daukar takardar zama dan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

DUBA WANNAN: Mun gano aikin da APC ke son Ganduje ya yi mata a zaben jihar Edo - PDP

Dangantakar da ke tsakanin Ajayi da gwamnan jihar, Oluwarotimi Akeredolu ta yi tsami yan watanni da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa Agboola da ubangidansa sun raba hanya ne kan yadda za a tafiyar da jihar sannan lamarin ya yi kamari ne a lokacin da Gwamna Akeredolu ya kaddamar da kudirinsa na sake tsayawa takara a karo na biyu.

A ranar Asabar, 20 ga watan Yuni, sabanin dake tsakanin gwamna Akeredolu da mataimakinsa ya sake daukar zafi, yayinda aka yi zargin ccewa Gwamna Akeredolu ya hana Agboola fita daga jihar Ondo da motocin gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng