Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1

Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1

- Jami'in NCDC a jihar Zamfara, J. Shalanga da wasu fitattun 'yan Najeriya sun rasu sakamakon annobar korona a yau Lahadi

- Sauran biyun sun hada da Hide Odekunle, tsohon shugaban LASIMRA da Farfesa Godwin Achinge na jami'ar jihar Benue

- Kafin rasuwar Achinge, shine mataimakin shugaban kwamitin ayyuka kan korona na jihar Benue

A yau Lahadi, 5 ga watan Yuli, korona ta kwashe rayukan 'yan Najeriya fitattu uku. Sun rasu ne sakamakon annobar korona.

Mutum ukun sun hada da Farfesa Godwin Achinge, J. Shalanga da Jida Odekunle wanda shine tsohon babban manajan LASIMRA.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi

Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1
Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1 Hoto: Vanguard da Nigerian Tribune
Asali: Depositphotos

Kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa, Achinge wanda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin ayyukan kan korona a jihar Benue, ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke Jos inda yake jinyar cutar sarkewar numfashin.

Wani mataimakin shugaban jami'ar jihar Benue ya tabbatar da kamuwar Achinge da cutar sa'o'i kadan kafin rasuwarsa.

A dayan bangaren, Shalanga, jami'in NCDC a Zamfara, wanda shine ke jagorantar yanayin yaduwar cutar a jihar ya rasu.

Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Kanoma ne ya tabbatar da mutuwar. Ya ce jami'in ya fara ciwon kafin a mika shi asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.

KU KARANTA KUMA: Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75

A bangaren Odekunle wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 53, ya rasu a cibiyar killacewa ta Onikan da ke jihar Legas.

Kafin rasuwarsa, shine Bobagunwa na Egbaland.

A halin yanzu, sama da mutum 28,000 ne a Najeriya suka kamu da cutar korona yayin da sama da mutum 11,000 suka warke.

A kalla an samu mutum 4,000 da suka harbu da kwayar cutar a makon da ya gabata. Wasu daga ciki sun hada da gwamnoni, hadimansu ko kuma 'yan uwansu.

Da yawa daga cikin wadanda suka kamu basu nuna wata alamar cutar ba kuma sun killace kansu kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bukata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng