Zaben Edo: Gwamna Wike zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP

Zaben Edo: Gwamna Wike zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP, a ranar Juma'ar da ta gabata, ya nada gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar Edo.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a kan shafinta na Twitter, inda ta bayyana gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin mataimakin kwamitin yakin neman zaben.

Wannan lamari ya faru ne kwana daya bayan da jam'iyyar APC ta nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar ta Edo.

Zaben Edo: Gwamna Wike zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP
Zaben Edo: Gwamna Wike zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP
Asali: UGC

A ranar Asabar, 19 ga watan Satumba na 2020, za a gudanar da zaben gwamna a jihar Edo, inda gwamna mai ci Godwin Obaseki, zai gwabza da dan takara na jam'iyyar APC; Osagie Ize-Iyamu.

Makonni kadan da suka gabata ne Gwamna Godwin Obaseki dai ya sauya sheka daga APC ya koma PDP kuma jam'iyyar ta tsayar da shi takara ba tare da wata-wata ba.

KARANTA KUMA: Abuja da jihohi 35 wanda cutar korona ta bulla a Najeriya

Idan ba a manta ba, Ize-Iyamu shi ne marikin tutar jam'iyyar PDP yayin zaben gwamnan Edo a shekarar 2016, yayin da kuma Obaseki ya tika shi da kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar APC.

Sashen Hausa na jaridar Premium Times ya ruwaito cewa, yanzu duk su biyu sun koma wa jam’iyyun da suka yi adawa a 2016.

Jerin sunayen baradan da za su fafata domin tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Edo sun hadar da;

Gwamna Ribas; Nyesom Wike (shugaban kwamitin yakin neman zaben)

Gwamnan jihar Adamawa; Umar Fintiri (shugaban kwamitin yakin neman zaben)

Atiku Abubakar.

Sanata David Mark.

Sanata Bukola Saraki.

Hon. Yakubu Dogara.

Sanata Enyinnaya Abaribe.

Sanata Ike Ekweremadu.

Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Peter Obi.

Sauran Gwamnonin PDP da suka hadar da:

Okezie Ikpeazu - Abia

Udom Gabriel Emmanuel - Akwa Ibom

Bala Muhammed - Bauchi

Duoye Diri - Bayelsa

Samuel Ortom - Benuwe

Benedict Ayade - Cross River

Ifeanyi Okowa - Delta

Dave Umahi - Ebonyi

Ifeanyi Ugwuanyi - Enugu

Oluwaseyi Makinde - Oyo

Aminu Waziri Tambuwal - Sakkwato

Darius Ishaku - Taraba

Bello Matawalle - Zamfara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel