Kotun daukaka kara ta tabbatar da Yahaya Bello a matsayin gwamnan Kogi
Kotun daukaka karar zaben gwamnan jihar Kogi da ke zamanta a Abuja, ta yi fatali da kararraki hudu da ke kalubalantar zaben Gwamna Yahaya Bello wanda ya mai do shi kujerar mulki a wa'adi na biyu.
Kotun a yayin zamanta da ta gudanar a ranar Asabar cikin birnin Abuja, ya tabbatar da nasarar Yahaya Bello a matsayin zababben gwamnanjihar Kogi.
Jam'iyyu hudu da suka kalubalanci sakamakon zaben ta hanyar shigar da korafinsu a gaban kuliya sun hadar da PDP (Peoples Democratic Party), APP (Actions People’s Party); SDP (Social Democratic Party) da kuma DPP (Democratic People’s Party).
Yayin zartar da hukunci daban-daban Alkalan kotun biyar karkashin Mai Shari’a Adamu Jauro, sun yi watsi da kararrakin hudu saboda rashin dalilai masu tushe.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, an yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, Musa Wada ya shigar, bayan ya gaza tabbatar da zarginsa na cewa an yi magudi a zaben.
Da yake zartar da hukunci, Mai Shari'a Muhammad Shu'aibu, ya yi fatali da korafin da jam'iyyar APP da DPP suka shigar na zargin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta cire sunayensu a zaben.
Kotun daukaka karar ta kuma yi watsi da karar neman soke zaben da 'yar takarar jam'iyyar SDP Natasha Akpoti ta shigar, yayin da ta gaza bayar da kwarararn hujjoji na zargin saba ka'idoji.
KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Najeriya ba za ta daina karbo bashi ba - Ministar Kudi
A karshe kotun ta nemi dan takarar jam'iyyar PDP; Musa Wada, da ya biya naira dubu 100 ga kowane daya daga cikin wadanda ya yi korafin a kansu da suka hadar da; Gwamna Bello, jam'iyyar APC da kuma hukumar INEC.
Ana iya tuna cewa, a zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a watan Nuwamba na shekarar 2019, Mista Bello ya lashe kuri'u 406,222 inda ya tika abokin karawarsa da kasa, na jam'iyyar PDP Mista Wada, da ya tashi da kuri'u 189,704.
'Yar takarar jam'iyyar SPD, Misis Akpoti, ta zo ta uku yayin da aka fidda sakamakon zaben inda ta samu kuri'u 9,482.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng