APC na yin kazamar siya - Saraki da Atiku sun musanta alaka da Hushpuppi

APC na yin kazamar siya - Saraki da Atiku sun musanta alaka da Hushpuppi

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana bayanin da ke danganta shi da wanda ake zargi da damfarar yanar gizo, Hushpuppi, wanda jam'iyyar APC tayi a matsayin kazamar siyasa.

Jami'an 'yan sanda a Dubai sun saki wani bidiyon yadda runduna ta musamman ta damke Hushpuppi a kan zargin damfarar N168 biliyan daga mutane 1.9 miliyan.

An kama shi a ranar 10 ga watan Yuni tare da wasu mukarrabansa 11 bayan aikata laifuka da suka hada da almundahanar kudade, damfarar banki da kutse.

A wata takarda da Yekini Nabena, mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa ya fitar a ranar Asabar, jam'iyyar ta bukaci bincikar wasu shugabannin PDP wadanda suka hada da Saraki.

APC na yin kazamar siya - Saraki da Atiku sun musanta alaka da Hushpuppi
APC na yin kazamar siya - Saraki da Atiku sun musanta alaka da Hushpuppi Hoto: Connet Abuja
Asali: UGC

An yi wannan kira ne saboda hoton da aka gani na Hushpuppi tare da Saraki da sauran jiga-jigan jam'iy PDP da suka hada sa Atiku Abubakar, Yakubu Dogara da Dino Melaye a Dubai.

A martanin da Saraki ya fitar ta hannun Yusuph Olaniyonu, ya zargi APC da saka siyasa mara ma'ana kuma kazama wacce ke nakasa yaki da rashawar da ake yi.

"Takardar da ta fito daga APC, jam'iyya mai mulki, na daya daga cikin hanyoyin da ke disashe kokarinta na yaki da rashawa da take yi," yace.

"Abinda ya kawo hakan kuwa shine yadda 'yan damfarar yanar gizo nan ke walwala tare da bayyana tarin dukiyarsu, APC bata ganin wani aibun hakan. A wannan lokacin, jam'iyyar bata yi kira ga wata cibiyar yaki da rashawa ba don bincikar su.

"Hakazalika, a lokacin da aka kama su bayan bata sunan 'yan Najeriya a idon duniya, babu abinda jam'iyyar mai mulki ta fito tace a kai.

"Lokacin da APC ta ga ya kamata tayi magana shine lokacin da tayi tunanin saka kazamar siyasa a al'amarin. A don haka muke kira ga jam'iyyar APC da ta guji yada karairayi da za su iya kawo rikici."

A wata takarda makamanciyar hakan, Paul Ibe, mai bai wa Atiku Abubakar shawara a kan yada labarai, ya ce mai gidansa bai yi taro da wanda ake zargin dan damfara bane. Hoto ne kawai wanda ya gibto.

"Muna shawartar jam'iyyar APC da Nabena su san irin kalaman da za su dinga fitarwa ba irin wadannan miyagun zargin ba," takardar tace.

KU KARANTA KUMA: Abin takaici ne haka uwargidata ke son ganin bayana - Mutumin da matarsa ta yankewa azzakari

"Da dai sun yi tunani, da sun gano cewa wannan al'amarin abun kunya ne ga kasar nan baki daya ba wai hanyar cimma manufar siyasa ba."

A ranar Juma'a, Hushpuppi, wanda asalin sunansa Raymond Abass, an gurfanar da shi a gaban wata kotun Amurka a kan zarginsa da damfara wacce za ta iya sa a yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari idan aka kama shi da laifi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel