Sabbin mutum 603 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Sabbin mutum 603 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 603 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.35 na daren ranar Asabar 4 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 603 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Sabbin mutum 603 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Sabbin mutum 603 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-135

Edo-87

FCT-73

Rivers-67

Delta-62

Ogun-47

Kaduna-20

KU KARANTA: Na kama matata a ƙarƙashin gadon kwartonta tsirara - Miji ya faɗa wa kotu

Plateau-19

Osun-17

Ondo-16

Enugu-15

Oyo-15

Borno-13

Niger-6

Nasarawa-4

Kebbi-3

Kano-2

Sokoto-1

Abia-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Asabar 4 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 28,167.

An sallami mutum 11,462 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 634.

A wani labarin daban da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya warke daga COVID-19 wato cutar korona.

Sakamakon gwajin da aka yi masa ranar Juma'a 3 ga watan Yuli ya nuna baya dauke da kwayar cutar.

Gwamnan ya killace kansa ne tun ranar 8 ga watan Yunin 2020 a lokacin da aka gano ya kamu da cutar.

Sanarwar warkewar gwamnan ta fito ne daga bakin Kwamishinan watsa labarai na jihar, Okiyi Kalu kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sanarwar ta ce, "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, gwajin da Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa, NCDC ta yi a kan samfurin Gwamna Okezie Ikpeazu a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020 ya fito a ranar Juma'a 3 ga watan Yulin 2020 kuma baya ɗauke da ƙwayar cutar.

Hakan na nufin Gwamna Ikpeazu ya warke daga cutar kamar yadda dokokin NCDC da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, suka tanadar.

Mun gode."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel