Boko Haram: Yadda sojin sama suka ragargaza sabbin shugabannin 'yan ta'adda

Boko Haram: Yadda sojin sama suka ragargaza sabbin shugabannin 'yan ta'adda

Dakarun sojin saman Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram masu tarin yawa da kayan aikinsu a harin da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai Mina, kusa da Gulumba da kuna yankin Gana-Kumshe a yankin arewacin jihar Borno.

Wannan ragargazar da dakarun suka yi wa mayakan ta'addancin ta hargitsa su tare da halaka sabbin shugabanninsu. Hakan ya faru ne a ranar 3 ga watan Yulin 2020.

Bayan rahotannin sirrin da rundunar sojin ta samu na wurin da mayakan suka koma da kuma inda kayan aikinsu suke, ta jiragen yaki dakarun suka tabbatar da ingancin zancen.

Babu jimawa sojojin suka dinga jefawa wuraren bama-bamai, lamarin da ya kawo halakar mayakan ta'addancin masu tarin yawa tare da wata bukkar kayan aikinsu wacce ta kama da wuta.

Wasu daga cikin mayakan da suka samu tserewa an bi su tare da halaka su.

Shugaban sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar , ya jinjinawa sadaukarwar ATF da kuma kwarewarsu.

Hedkwatar tsaro ta kasa, ta kara da kira garesu da su tsananta takura 'yan ta'addan tare da duk wani nau'in ta'addanci da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar nan.

Boko Haram: Yadda sojin sama suka ragargaza sabbin shugabannin 'yan ta'adda
Boko Haram: Yadda sojin sama suka ragargaza sabbin shugabannin 'yan ta'adda. Hoto daga Defense Headquarter
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci

A wani labari na daban, hukumar mayakan saman Najeriya ta samu sabon jirgin yakin leken asiri mai suna ATR-42 a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.

Mai magana da yawun hukumar, Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki a shafin yanar gizo.

Jawabin yace: "Bisa ga cigaba da kokarin tabbatar da cewa ana samun labaran leken asiri domin yakin yan ta'adda a yan tada zaune tsaye a fadin tarayya, hukumar Sojin Najeriya a yau 3 ga Yuli, 2020, ta samu sabon gyararren jirgi, ATR-42 (NAF 930).

"Shugaban shirye-shiryen hukumar, AVM Oladayo Amao ya karbi sabon jirgi madadin babban hafsan hukumar, AM Sadiqque Abba, a tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja yayinda shi babban hafsan yake Arewa maso gabas domin lura ga atisayen Operation LONG REACH II."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel