An yi wa wani jirgin UN ruwan harsashi a Borno

An yi wa wani jirgin UN ruwan harsashi a Borno

An bude wa wani jirgi mai saukan ungulu mallakar Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) wuta a Damasak, a karamar hukumar Mobbar da ke arewacin jihar Borno.

Duk da haka, jirgin ya lallaba ya dawo sansaninsa a Maiduguri jim kadan bayan harin da aka kai masa a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020.

UNHAS na taimakawa ne wurin rabon abinci da karkashin shirin samar da abinci na duniya a yankin.

An kai wa helicoftar UN hari a Borno
An kai wa helicoftar UN hari a Borno. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

HumAngle ta ruwaito cewa an kai hari a jihar Borno, kwana guda bayan Gwamnan jihar, Babagana Zulum ya jogoranci wata tawaga zuwa Damasak don raba wa fiye da gidaje 12,000 tallafin abinci.

KU KARANTA: Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai – Majiya daga Rundunar Soji

A halin yanzu dai ba a tabbatar idan kungiyar ta'adanci ta (ISWAP) ce ta kai wa matafiya da ke cikin jirgin harin ba.

ISWAP ta amsa cewa ita ce ta kai harin na Damasak a tashan Amaq da ta saba amfani da shi wurin wallafa ayyukan ta tare da kira ga mutane su shiga su tallafa mata.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar jirgin, UNHAS, da aka kai wa harin fari ne da tambarin UN a jikinsa kuma samfurin Bell 412 da 212 ne da aka tura yankin domin ayyukan jin kai.

A wani labarin daban, kun ji cewa wata majiya daga rundunar sojojin Najeriya ta ce Boko Haram suna samun makamai da motocci ne yayin harin da suke kai wa sansanin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta bayyana hakan ne yayin mayar da martani a kan ikirarin da kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya yi na cewa rundunar soji ba ta san wadanda ke daukan nauyin 'yan ta'adda ba da inda suke samo makamai.

"Ba gaskiya bane a ce makaman da 'yan ta'addan ke amfani da shi yana da banbanci da wadanda muka siyo," a cewar daya daga cikin majiyar.

"Maganar gaskiya shine mafi yawancin motocin, tankunan yaki da sauran makamansu daga sansanin mu suka sace. Idan kana iya tunawa, su kan sace makamai daga sansanin mu da suka kai hari. Yawancin motocin da suke amfani da shi daga wurin dakarun mu suka sace.

"Kuma suna samun makamai daga kasashen da muke makwabtaka da su na kusa da yankin tafkin Chadi a farashi mai rahusa. Safarar makamai daga yankin Tafkin Chadi yana da sauki saboda rashin tsaro a iyakoki," in ji majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel