Badakala: An bankado wata makarantar FG da ake biyan mai shara albashin N32m

Badakala: An bankado wata makarantar FG da ake biyan mai shara albashin N32m

Babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya ya ce ya bankado wata badakala a tsarin kashe kudi a makarantar horon lauyoyi ta Najeriya.

Rahoton binciken da aka mikawa majalisar dattijai ya samu mahukuntan makarantar da laifin tafka almundahana da kashe kudade babu kasafi balle samun sahalarewar gwamnati.

Yanzu haka kwamitin majalisar dattijai ya na nazari tare da gudanar da bincike a kan rahoton binciken da aka gudanar tun a shekarar 2015.

A cewar rahoton, a tsawon watanni goma sha biyu, hukumar makarantar ta saka zunzurutun kudi da yawansu ya kai miliyan N32 a asusun wani mai shara da ba a ambaci sunansa ba.

Kazalika, ofishin babban mai binciken ya bankado yadda hukumar makarantar ta biya wasu ma'aikata 52 N36m a matsayin kudin sutura, kuma an tura kudin ne asusun wani ma'aikaci guda daya, lamarin da ya sabawa dokar Najeriya ta biyan ma'aikata hakkokinsu.

Wani bangare na rahoton ya bayyana cewa; "nazarin hada - hadar kudi a makarantar horon lauyoyi ya nuna cewa hukumar makarantar ta biya wasu ma'aikatanta N36m a matsayin kudin sutura a iya shekarar 2013.

"Hukumar makarantar ta gaza gabatar da wata shaidar samun izini daga hukumar albashi wacce ta bata damar biyan irin wadannan kudaden zuwa asusun ma'aikata, kuma babu bayanan cewa an yi kasafi kafin kashe kudaden."

Badakala: An bankado wata makaranatar FG da ake biyan mai shara albashin N32m
Hedikwatar makarantar horon lauyoyi da ke Abuja
Asali: UGC

Ganin an fara yi wa hukumar makarantar tonon silili daga sashe binciken kwakwaf na ofishin babban mai bincike, sai shugaban makarantar, Farfesa Isa Hayatu Chiroma, ya fito ya bayyana cewa ba ya kan karagar mulki lokacin da aka tafka waccan badakala.

DUBA WANNAN: Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda

Sai dai, ya nuna amincewarsa a kan cewa shi aikin gwamnati a tsare ya ke, kuma akwai ka'idoji da sharudan aikata kowanne al'amari.

Mambobin kwamitin majalisar dattijai da ke binciken rahoton badakalar sun amince cewa ba a karkashin shugabancin Chiroma aka tafka waccan badakalar kudi ba.

Sai dai, duk da hakan, kwamitin binciken ya umarci Chiroma ya kwato dukkan wadancan kudade tare da mayar da su asusun makarantar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel