Edo 2020: NYSC ta bai wa Obaseki sabon satifiket

Edo 2020: NYSC ta bai wa Obaseki sabon satifiket

National Youth Service Corps (NYSC) ta bai wa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo sabuwar takardar shaidar kammala hidimar kasa bayan kuskuren da tayi a ta farko.

Gwamnan ya hidimtawa kasa karkashin hukumar a 1980, amma kuma an samu kuskure a satifiket din da aka bashi.

An cire harafi daya daga cikin satifiket din inda aka rubuta Obasek a maimakon Obaseki.

A yayin tantance masu bukatar takara karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben gwamnoni na jihar Edo na 2020, an gano wannan kuskuren wanda hakan ya zamo daya daga cikin dalilan da suka sa aka hana shi takara.

Daga bisani, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP inda ya fito takara kuma ya lashe zaben fidda gwani.

Kafin zaben fidda gwanin da aka yi na jam'iyyar PDP a ranar 25 ga watan Yuni, ya rubuta wasika ga hukumar inda ya bukaci a gyara masa kuskuren sannan a bashi sabuwar shaida.

A wasika mai kwanan wata 19 ga watan Yunin 2020, wacce jaridar The Cable ta gani, Okonofua K N, wanda ya sa hannun a madadin darakta janar din hukumar, ya ce sun yi bincike a kai.

Edo 2020: NYSC ta bai wa Obaseki sabon satifiket
Edo 2020: NYSC ta bai wa Obaseki sabon satifiket. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu

Ya tabbatar da cewa akwai bukatar sauya wa gwamnan satifiket din kacokan wanda zai kwashe dukkan haruffan sunansa.

"Game da wasikar ku mai lamba EOG/ABI/99/VOL IV/172 mai dauke da kwanan wata 18 ga Yunin 2020, da bukatar da kuka rubuta a sama," wasikar tace.

Ta kara da cewa, "An umarceni da in sanar da ku cewa bayan bincike da aka yi, hukumar ta amince da bada sabon satifiket mai dauke da suna OBASEKI mai lamba 063107 dauke da kwanan wata 6 ga Augustan 1980 mai cikakken haruffan sunansa.

“Darakta janar na hukumar na mika gaisuwarsa."

Obaseki zai kara da Osagie Ize-Iyamu a ranar 19 ga watan Satumban 2020 wurin zaben kujerar gwamnan.

ya kayar da Ize-Iyamu a shekarar 2016 yayain da yayi takara a karkashin jam'iyyar PDP.

An zaba Gwamna Godwin Obaseki ne a karkashin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel