Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya sallami hadiminsa

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya sallami hadiminsa

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya sallami babban mataimakinsa na musamman a kan tsaro mai kula da karamar hukumar Kaba Bunu, Ayo Ariyo.

Ya kuma amince da nadin Mohmoh Abdul Lasisi a matsayin mataimakinsa domin maye gurbin marigayi Hon. Suleiman Abdulateef Adinoyi.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr Mrs Folashade Ayoade Arike ce ta sanar da sallamar hadimin da sabbin nadin a cikin sanarwar da ta fitar a daren ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya sallami hadiminsa
Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya sallami hadiminsa. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

Olorunleke Moses ne zai maye gurbin Ariyo wanda a baya shine babban mataimakin gwamna na musamman a kan harkokin siyasa na mazabar Kabba /Ijumu ta tarayya.

Moses kuma shine tsohon shugaba mai kula da karamar hukumar Kabba/Bunu.

Adeyemi Olabode John zai kama aiki a matsayin babban mai bawa gwamna shawara na musamman a kan harkokin siyasa a mazabar Kabba/Bunu ta tarayya.

Sanawar ba ta bayyana dalilin sallamar Ayo Ariyo daga aiki ba sai dai ta ce dukkan wadanda aka nada za su fara aiki nan take.

KU KARANTA: An kama wani mutum da ya yi wa 'yarsa ciki a Adamawa

A wani labarin daban kun ji cewa a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya caccaki dattawan arewa inda ya zargesu da mayar da yankin baya a maimakon tabbatar da ci gabanta.

Da yake magana a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin gidauniyar tunawa da Ahmadu Bello karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Bello ya ce shugabannin yankin da suka zo bayan Ahmadu Bello sun ki dorawa daga inda ya tsaya.

Gwamna Bello ya zargi shugabannin da kunna wutar rikici na kabila da addinai wanda ya hana yankin zaman lafiya tare da kawo zubar jini.

Ya ce duk da yankin ta samar da manyan masu kudi, har yanzu yankin ne koma baya saboda yadda jama'ar suka ki saka hannun jari tare da shigewa gaba ta bangaren kawo ci gaba.

A don haka ya yi kira ga dattawan yankin da su yi koyi da hallayar Sardauna don ci gabanta. "Marigayi Ahmadu Bello yana nuna daidaito da rashin boye-boye a shugabancinsa.

"A saboda haka ne ya samu ci gaba mai tarin yawa sannan ya kafa martabar jama'ar arewa a idon duniya.

"A takaice, rashin gaskiya a tsakanin shugabannin yankin ya zama babban matsala wurin hana ci gaban yankin.

Yadda za a shawo kan matsalar shine koyi da nagartar Sardaunan Sokoto wanda ya yi watsi da kabilanci ko banbancin addini," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel