Coronavirus: Jihohi 20 da suka zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin bana

Coronavirus: Jihohi 20 da suka zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin bana

Jihohi da dama a faɗin ƙasar sun sake yin bitar kasafin kudinsu na bana, domin daidaita shi da hakikain yanayin tattalin arziki wanda annobar cutar korona ta haifar.

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa, akalla jihohi 20 a fadin tarayya sun zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin da suka shigar cikin doka a baya.

A watan Afrilun da ya gabata ne, jaridar ta ruwaito cewa, annobar korona tana barazana ga jimillar kasafin kudi na naira tiriliyan 9 wanda duk jihohin kasar suka shigar cikin doka.

A halin yanzu, wannan lamari ya tilasta wa galibin jihohin jingine wasu manyan ayyuka da suka kudirci aiwatar wa da kuma dakatar da biyan sabon mafi karancin albashi.

Wasu jihohin kuma sun zatfare wani kaso daga cikin albashin ma'aikatansu da na masu rike da mukaman siyasa.

Coronavirus: Jihohi 20 da suka zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin bana
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Coronavirus: Jihohi 20 da suka zaftare naira tiriliyan 1.4 daga kasafin kudin bana Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Trust
Source: UGC

Alal misali jihar Gombe, ta sanar da dakatar da biyan sabon mafi karancin albashi na naira dubu 30, tare da rage albashin dukkan masu rike da mukaman siyasa da kashi 25 cikin dari.

Hakan kuma take a jihar Adamawa, inda gwamnatin jihar ta daina biyan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatanta.

Dangane da girman adadin da aka rage, jihar Legas ta fi kowace jiha a duk fadin kasar yayin da ta zaftare naira biliyan 248 daga kasafin kudin bana na naira tiriliyan 1.168.

Jihar Ribas ta rage kashi 48 cikin 100 daga kasafin kudinta na bana, inda kwamishinan kudi na jihar, Issac Kamalu, ya ce an takaice shi zuwa naira biliyan 300 bayan sassabe naira biliyan 230 daga cikin naira biliyan 530.

Shi ma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya zaftare kashi 26 cikin 100 na kasafin kudinta, biyo bayan rage naira biliyan 47 daga cikin naira biliyan 178.6 da a baya ta shigar cikin doka.

KARANTA KUMA: Buhari ya sake sabunta nadin jakadu 12 - Garba Shehu

Duba da durkushewar tattalin arziki da annobar korona ta haifar, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da shirinsa na zaftare kashi 30 cikin daga kasafin kudin jihar.

A jihar Yobe, gwamna Mai Mala Buni, ya yi bitar kasafin jihar, inda ya sassabe shi daga naira biliyan 108 zuwa naira biliyan 86.

Gwamnatin Benuwe karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom, ta rage naira biliyan 70 daga naira biliyan 189 na kasafin kudin jihar da ta shigar cikin doka.

Hakan ta ke kuma ga sauran jihohi kamar Ekiti, Kaduna, Sakkwato, Delta, Bauchi, Katsina, Filato, Imo da sauransu.

Yayin da mafi akasari, a kwaskwarimar da gwamnatocin suka yi wa kasafin kudin jihohinsu, ba a samu wadda ta rage kasafin kudin sashen ilimi ba, inda da dama kasafin sashen kiwon lafiya ya karu.

Jerin jihohi 20 da suka yi wa kasafin kudin jiharsu kwaskwarima sun hadar da: Adamawa; Anambra; Akwa Ibom; Bauchi; Benuwe; Delta; Ekiti; Ebonyi; Jigawa; Imo; Kaduna; Kano; Katsina; Kwara; Kogi; Legas; Neja; Filato; Ribas; da Sakkwato.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel