Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero

Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero

Shugaban kamfanin jirgin saman Aero Contractors, Ado Sanusi, ya shawarci fasinjojin dake fama da mura ko zazzabi kada su zo tashar jirgin sama saboda gudun abinda ka iya biyo baya idan sukayi atishawa.

Yayinda yake jawabi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV, ranar Alhamis, Sanusi yace za'a killace duk wanda yayi atishawa cikin jirgin saboda za'a daukeshi mai cutar Korona.

Yace: "Ina son bayyanawa mutane cewa idan kanada ciwon zazzabin sauro ko mura, kada ka zo tashar jirgin sama saboda akwai yiwuwan a hanaka shiga cikin jirgi."

"Wannan shine sabon halin da muka samu kanmu."

"Abu mafi muhimmanci ga kamfanonin jiragen sama shine su tabbatar da cewa jiragensu na tsaftace kuma abinda mukeyi kenan."

"Saboda haka idan muka ga mutum yana atishawa, zamu daukeshi fasinja mai Korona... Zamu killaceshi har sai mun mikashi ga jami'an lafiyan tashar jirgin saman."

Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero
Duk wanda yayi atishawa cikin jirginmu kawai zamu daukeshi mai Korona - Aero
Asali: Instagram

Ado Sanusi ya kara da cewa ba za'a amince wani fasinja ya shiga jirgi ba don ya gabatar da takardar shaidar Likita cewa yana da zazzabi.

"Kamfanin Jirgina ba zai amince wani fasinja da ya kawo takardar shaidar Likiti cewa yana dauke da Malariya ya shiga jirgi ba. Na gwammace ya gabatar da takardar gwajin cutar Korona ya nuna cewa bai dauke da cutar."

"Idan kana da zazzabi, kawai ka zauna a gida. Idan ka samu sauki, za ka iya tafiya." Ya ce

KU KARANTA: Babu rikici ko baraka a APC - Tinubu bayan karban bakuncin shugabannin kwamitin rikon kwarya

Shugaban kamfanin jirgin ya kara da cewa kamfaninsa za ta daina raba kayan abinci cikin jirgi kamar yadda aka saba.

"Ba zamu raba abinci cikin jirgi ba saboda hakan zai yawaita haduwar ma'aikata da fasinjoji kuma Fasinjoji zasu bukaci cire takunkumin fuska kafin iya cin abinci. Saboda hakan ban tunanin ya dace muyi." Yayi bayani

A ranar Laraba, ministan sufurin sama, Hadi Sirika, ya sanar da cewa jiragen sama za su kama bakin aiki a Legas da Abuja fari daga ranar 8 ga Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel