Hotuna: Aisha Buhari a wurin ta'aziyar surikar Ganduje, Florence Ajimobi
Mrs Aisha Buhari, matar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ziyarci Florence Ajimobi, matar tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a ranar Laraba a Legas.
The Punch ta ruwaito cewa A'isha Buhari ta isa gidan da ke Glover Road, Ikoyi Legas ne a safiyar ranar Laraba.
Mrs Buhari bayan yabawa halayen tsohon jigon na jam'iyyar ta APC ta yi wa iyalansa jajen rashinsa.

Asali: UGC

Asali: UGC
Ta bukaci iyalan nasa su rungumi ƙaddara tunda Allah ya san dalilin da yasa ya karɓi ransa a yanzu.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Kwamitin riko na APC ya ziyarci Tinubu a gidansa (Bidiyo)

Asali: UGC
Sauran wadanda suka ziyarci gidan na marigayi Ajimobi tare da A'isha sun hada da Olufunso Amosun, matar tsohon gwamnan jihar Osun, Ibikunle Amosun; Bolanle Amobode, matar tsohon gwamnan Legas Akinwumi Ambode.
Sai kuma Sherifat Aregbesola, matar tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola; da Ibijoke Sanwo-Olu, matar gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng