2023: Shehu Sani, Dangiwa da sauransu sun yi martani a kan yunkurin kafa sabuwar jam'iyya

2023: Shehu Sani, Dangiwa da sauransu sun yi martani a kan yunkurin kafa sabuwar jam'iyya

Wasu fitattun 'yan Najeriya uku da aka bayyana sunayensu a cikin 'yan gwagwarmayar da ke yunkurin kafa sabuwar jam'iyya sun ce ba a tuntubesu ba kafin a fitar da sanarwa.

Fitattun mutanen; Abubakar Dangiwa Umar; tsohon kanal a rundunar soji da ya birkice ya koma dan gwagwamarya, Sanata Shehu Sani; tsohon mamba a majalisar dattijai mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, da tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa; Olisa Agbakoba, sun ce ba a tuntubesu ba kafin fitar da sanarwar kafa kungiyar NCF (National Consultative Forum).

Dangiwa da Shehu sun yi magana da jaridar Premium Times yayin da Mista Agbakoba ya fitar da jawabi.

A ranar Laraba ne kafafen yada labarai su ka wallafa rahoton cewa wasu fitattun 'yan gwagwarmaya 30 da suka hada da malaman jami'o'i da sauran kwararru da 'yan gwagwarmaya sun fara yunkurin kafa sabuwar jam'iyya kafin babban zaben shekarar 2023.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Anthony Kila ya fitar zuwa kafafen yada labarai na kasa.

A cewar Farfesa Kila, an kafa kungiyar NCF bayan shafe wata guda ana gudanar da taro da tuntuba ta kafofin zamani.

Mambobin kungiyar, kamar yadda aka lissafosu a cikin sanarwar, sun hada da tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN); Obadiah Mailafia, Mista Agbakoba, Femi Falana, Mista Abubakar Dangiwa Umar.

Sai tsohuwar minista; Oby Ezekwesili, Jibrin Ibrahim, Yabagi Sanni, Nkoyo Toyo, Isa Aremu, Chidi Odinkalu, da Shehu sani.

Ragowar sun hada da Remi Sonaiya, Tanko Yinusa, Shettima Yerima, Funke Awolowo, Peter Ameh, Lanre Banjo da sauransu.

Da Premium Times ta tuntubi Dangiwa Umar ya bayyana cewa duk da akwai bukatar samun irin wannan kungiya, ba a tuntube shi ba kafin saka sunansa a matsayin mamba.

2023: Shehu Sani, Dangiwa da sauransu sun yi martani a kan yunkurin kafa sabuwar jam'iyya
2023: Shehu Sani, Dangiwa da sauransu sun yi martani a kan yunkurin kafa sabuwar jam'iyya
Asali: UGC

"Ba a tuntubeni ba, kawai na ga sunana a cikin kungiyar," a cewar Kanal Dangiwa Umar mai ritaya.

Kazalika, Shehu Sani ya bayyana cewa ya yarda akwai bukatar fara irin wannan gwagwarmaya, ba a tuntube shi ba kafin a saka sunansa.

DUBA WANNAN: Sunaye: Buhari ya dakatar da shugaba, darektoci 4 da manyan ma'aikata 8 a hukumar NSITF

Dukkan fitattun mutanen sun bayyana cewa su na ganin girman sauran mambobin da ke cikin kungiyar.

A cikin wani jawabi da Mista Agbakoba ya fitar ranar Alhamis, ya musanta zama mamba a cikin sabuwar kungiyar NCF.

Duk da fitaccen lauya Falana bai ce komai ba da aka tuntube shi, wani makusancinsa ya ce ba a tuntube shi ba kafin a saka sunansa a cikin sabuwar kungiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng