Sunaye: Buhari ya dakatar da shugaba da darektoci hudu a hukumar NSITF

Sunaye: Buhari ya dakatar da shugaba da darektoci hudu a hukumar NSITF

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da manajan darektan hukumar kula da asusun kudin lamuni da ake warewa domin walwalar 'yan Najeriya (NSITF), Mista Adebayo Somefun.

Kazalika, shugaba Buhari ya amince da dakatar da wasu darektoci guda hudu a hukumar.

Darektocin da shugaba Buhari ya amince da dakatar da su sun hada da; Mista Jasper Ikedi Azusalam (darektan kudi da saka hannun jari), Uwargida Olukemi Nelson (darektan aiyuka), da Alhaji Tijjani Darazo Sulaiman (darektan gudanarwa).

Sanarwar dakatar da Somefun da darektocin na kunshe ne a cikin wani jawabi da Charles Akpan, mataimakin darektan yada labarai da hulda da jama'a a ma'aikatar kwadago da samar da aiyuka, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Bayan darektocin, shugaba Buhari ya amince da dakatar da wasu ma'aikatan hukumar da sua=ka hada da; Mista Olusegun Olumide Bashorun, Mista Lawan Tahir, Mista Chris Esedebe, Mista Olodotun Adegbite.

Sauran sun hada da da; Mista Emmanuel Enyinnaya Sike, uwargida Olutoyin O. Arokoyo, Dorathy Zajeme Tukura, da uwargida Victoria Ayantuga.

Jawabin ya bayyana cewa an dakatar da ma'aikatan ne bayan wani sakamakon bincike ya samesu da aikata laifuka ma su nasaba da almundahanar kudi da cuwa-cuwar kwangiloli.

Ana tsammanin ma'aikatan za su fuskanci wani kwamitin bincike na hadin gwuiwa domin amsa tambayoyi a kan zarginsu da saba dokoki da ka'idojin aiki daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Sunaye: Buhari ya dakatar da shugaba da darektoci hudu a hukumar NSITF
Shugaba Buhari
Asali: Twitter

An umarci ma'aikatan da dakatarwar ta shafa su mika ragamar gudanar da aiyukan ofisoshinsu ga manyan jami'an da ke bangarensu.

DUBA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, ya rantsar da sabon shugaban hukumar tabbatar da daidaito a rabon mukamai da guraben aiyukan gwamnatin tarayya (FCC), Muheeba Dankaka daga jihar Kwara, da kuma wasu mambobin hukumar su 36.

Shugaban kasar ya kuma rantsar da Kwamishinonin tarayya na hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC) su shida, ciki harda Gboyega Oladele daga Osun.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Buhari ya kuma rantsar da sabbin sakatarorin dindindin su hudu da kuma mambobin hukumar kula da ma’aikatan gwamnati (FCSC) su biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel