Ganduje ya karasa janye dokar kulle a jihar Kano

Ganduje ya karasa janye dokar kulle a jihar Kano

Gwamman jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da karasa janye dokar kulle da aka saka tun watan Afrilu bayan bullar annobar korona a jihar.

Ganduje ya sanar da hakan ne a yau, Alhamis, yayin da ya ke jawabi a wurin taron da ya saba gudanarwa wanda yanzu haka ake yinsa a fadar gwamnatin jihar Kano.

A cikin watan Yuni ne gwamna Ganduje ya kara kwanaki biyu a kan ranakun Juma'a da Lahadi da ake sassauta dokar kulle a jihar Kano.

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta sake fitar da jerin wasu matakan sake sassauta dokar kulle a fadin Najeriya.

Daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka akwai umarnin bude makarantun firamare da sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa kammala karatu.

Ganduje ya karasa janye dokar kulle a jihar Kano
Ganduje
Asali: Facebook

Kazalika, gwamnatin tarayya ta janye dokar dakatar da zirga - zirgar mutane da ababen hawa a tsakanin jihohi.

Tuni aka bude manyan tashohin mota domin jigilar mutane da kayayyaki a tsakanin jihohi bayan dawowar harkokin sufuri ta motoci wacce aka shafe kusan wata uku da takatarwa.

A cikin wata sanarwa da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya fitar da yammacin ranar Laraba, ya ce jirage za su fara tashi da sauka a iya cikin gida Najeriya a Abuja, Legas, Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri.

A cewar Sirika, jirage za su fara tashi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas da filin jirgin sama na Nmamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 8 ga watan Yuli, 2020.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fadi hukumomin da ke da alhakin bayyana ma su daukar nauyin Boko Haram

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano da filin jirgin sama na Fatakwal a jihar Ribas da na Maiduguri a jihar Borno za su fara aiki daga ranar 11 ga watan Yuli.

Sauran filayen jirgin sama na kasa za u koma aiki daga ranar 15 ga watan Yuli, kamar yadda ministan ya bayyana.

Kazalika, Sirika ya ce za a sanar da ranar dawowar tashi da saukar jiragen kasa da kasa nan gaba, ya bukaci jama'a su kara hakuri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel