Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare

Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da dakatar da shugaban karamar hukumar Misau tare da mataimakinsa da sakataren karamar hukuma.

Mohammed ya dauki matakin dakatar da shugabancin karamar hukumar Misau ne bayan barkewar wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, a kauyen Zadawa da ke karkashin karamar hukumar.

Da ya ke sanar da dakatar da shugabannin yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Mohammed ya ce za a nada shugaban riko da zai rike karamar hukumar Misau.

Ya dauki alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta yi jinkiri wajen daukan tsauraran matakai domin kiyaye afkuwar makamancin irin wannan mummunan rikici a nan gaba.

"Bayan mun karbi rahoton abinda ya faru, mun ga akwai bukatar mu dauki matakai ma su tsauri domin ganin ba a kara samun irin wannan mummunan rikici ba a nan gaba.

"Mun san wutar irin wannan rikici ta na nan ta na ruruwa a wasu kananan hukumomin, a saboda haka dole mu yi wa tufkar hanci tun yanzu.

Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma, mataimakinsa da sakatare
Bala Mohammed Kauran Bauchi
Asali: Twitter

"Amma, yanzu a kan faruwar wannan rikici, mun yanke shawarar dakatar da shugaban riko na karamar hukumar Misau tare da mataimakinsa da sakataren karamar hukumar, mun nada sabon shugaba, Isa Kufai, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Toro ne," a cewar Mohammed.

DUBA WANNAN: Suna da jiha : Buhari ya sake aikawa majalisa sabbin sunayen mutane 42 a matsayin jakadu

Sannan ya cigaba da cewa; "na umarci kwamishinan 'yan sanda da kwamandan rundunar NSCDC su jagoranci tawagar rundunar jami'ansu zuwa Misau domin tsaurara matakan tsaro na tsawon wani lokaci.

"Mun tattauna da ma su ruwa da tsaki, mai martaba sarkin Misau, hakimi, shugabannin kungiyoyin makiyaya da jami'an tsaro domin tattauna kiyaye faruwar irin wannan mummunan rikici a nan gaba.

"A saboda haka, na kafa wani kwamitin bincike mai mambobi 13 a karkashin jagorancin Tijani Baba Gamawa domin sake zurfafa bincike, za su mikawa gwamnati rahoto a cikin sati uku."

A wani rahoto da hukumar kasa da kasa da ke sa ido a kan rigingimu ta fitar a shekarar 2018, ta ce rikicin makiyaya da manoma ya sha gaban rikicin kungiyar Boko Harama a asarar rayukan jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel