Damfara: An kama wani mutum yana siyarwa 'yan gudun hijira fom din bogi na N-Power

Damfara: An kama wani mutum yana siyarwa 'yan gudun hijira fom din bogi na N-Power

- Jami'an tsaro sun kama wani mutum yana siyarwa 'yan gudun hijira fom din bogi na N-Power

- Wanda ake zargin ya damfari mutum 44 cikin 'yan gudun hijirar kafin tonuwar asirinsa a ranar Laraba

- Kakakin NSCDC, DSP James Bulus, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce suna tuhumar mutumin

Hukumar NSCDC tare da hadin guiwar hukumar sansanin 'yan gudun hijira ta Bakassi, ta damke wani mai suna Ibrahim Mohammed, wanda ake zargi da siyar da fom din N-Power ga 'yan gudun hijira dake karamar hukumar Guzamala a kan N10,000.

An gano cewa wanda ake zargin ya damfari mutum 44 cikin 'yan gudun hijirar kafin tonuwar asirinsa a ranar Laraba.

Kamar yadda daya daga cikin wadanda aka damfarar mai suna Musa Ali ya sanar, ya biya N5,000 tare da abokinsa

Damfara: An kama wani mutum yana siyarwa 'yan gudun hijira fom din bogi na N-Power
Damfara: An kama wani mutum yana siyarwa 'yan gudun hijira fom din bogi na N-Power Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Lamarin ya fara ne a ranar Litinin inda ya sanar da mu cewa an fara diban aikin N-Power kuma fom N5,000.

"Mutum a kalla 40 suka biya kudin kafin su kai wa hukumar sansanin rahoton. A nan ne aka sanar da mu kyauta ne kuma damfarar mu aka yi.

"A kalla ya tara kudin da suka kai N100,000 daga wurin jama'a. Daga nan ne muka nuna kamar bamu sani ba tare da kiransa don yi wa wasu rijista.

"Daga nan kuwa jami'an tsaro suka damke shi," Zanna yace.

Jami'an sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi sun tabbatar da wannan ci gaban, sun ce ana zarginsa da shiga sansanin ne ta hanyar hada baki da wasu 'yan sansanin.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade

"Eh, gaskiya ne. An kama shi tun jiya tare da hadin guiwar jami'an SEMA da NEMA a sansanin.

"Yana damfarar jama'a daga 1000 zuwa 7000. A halin yanzu yana hannun NSCDC a Maiduguri inda ake tuhumarsa.

"A garemu, wannan babbar mugunta ce da har mutum zai iya damfarar 'yan gudun hijira," wani jami'i a sansanin ya sanar duk da ya nemi a sakaya sunansa.

A yayin da aka tuntubi kakakin NSCDC, DSP James Bulus, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce suna tuhumarsa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel