Niger Delta: Kungiyoyi 13 na 'yan tada kayar baya sun aikewa Buhari muhimmin sako

Niger Delta: Kungiyoyi 13 na 'yan tada kayar baya sun aikewa Buhari muhimmin sako

Kungiyoyi 13 na tsoffin tsagerun Neja Delta wadanda suka amince da janye takobinsu a karkashin shirin gwamnatin tarayya na rangwame, suna barazanar komawa ruwa, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kungiyoyin, karkashin Coalition of Niger Delta Agitators (CNDA), sun ce sun janye yarjejeniyar da aka yi tsakaninsu da gwamnatin tarayya saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki cika musu bukatunsu.

A wata takardar da shugabannin kungiyoyin 13 suka fitar sun ce Buhari na ci gaba da kin sauraron kiran da suke masa na sallamar ministan kula da al'amuran yankin, Sanata Godswill Akpabio tare da kin sallamar kwamitin rikon kwarya na kula da ci gaban su.

Niger Delta: Kungiyoyi 13 na 'yan tada kayar baya sun aikewa Buhari muhimmin sako
Niger Delta: Kungiyoyi 13 na 'yan tada kayar baya sun aikewa Buhari muhimmin sako Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Shugabannin kungiyoyin sune; Janar John Duku na Niger Delta Watchdogs, Janar Ekpo Ekpo a madadin Niger Delta Volunteers, Janar Osarolor Nedam a madadin Niger Delta People's Fighters, Manjo janar Henry Okon Etete a madadin Niger Delta Warriors da sauransu.

Kungiyar ta CNDA ta kuma yi Allah wadai da halin shugaban kasar na kin magance lamuran wariya da ake nunawa yankin Neja Delta ta bangaren nade-nade a ma’aikatar man fetur da gas.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade

Musamman maye gurbin manajan darakta na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) da wani a yankin.

"CNDA ta janye yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninta da gwamnatin tarayya. Kungiyar ta bukaci gaggauta tsige ministan kula da harkokinta tare da maye gurbin shugaban NNPC da wanda ya dace daga yankin amma mun ji shiru.

"Daukacin CNDA sun yi Allah wadai da irin halin da gwamnatin tarayya ke nuna mata karkashin shugabancin Muhammadu Buhari. Gwamnatin na ci gaba da nuna halin ko-in kula ga dukkan koke-koken 'yan yankin Neja Delta.

"Abun takaici ne yadda gwamnatin nan ke cewa bata amince da rashawa ba bayan dumbin zargin rashawa da ake wa wasu ma'aikatu, sashe da cibiyoyi amma tayi shiru.

"Abinda mulkin shugaba Buhari ke yi wa yankin na so ya dawo da abubuwan da suka faru a tsakanin 2005 zuwa 2009, wanda ya tada hankalin kasar nan kafin kokarin marigayi Yar'adua.

"Kada a daura wa CNDA laifi a kan duk abinda aka gani nan gaba. Zai biyo baya ne saboda rashin kokarin shugaba Buhari na shawo kan matsalolin da ta mika garesa," kungiyar tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel