Sunaye: Buhari ya sake aikawa majalisa sabbin sunayen mutane 42 a matsayin jakadu
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nemi amincewar majalisar dattijai domin ta tabbatar da sunayen mutane 42 da ya ke son kara nadawa a matsayin jakadun Najeriya a kasashen ketare.
Daya daga cikin mutanen da shugaba Buhari ya aika sunansu zai kasance jakada mai cikakken iko a yayin da sauran mutanen 41 za su kasance jakadu na wucin gadi.
Daga cikin jakadun da za a nada akwai tsohon minista daga jihar Legas; Ademola Seriki, Debo Adesina daga jihar Oyo, Dare Sunday-Awoniyi daga jihar Kogi, da sauransu.

Asali: Facebook
Ga cikakken jerin sunaye da jihohin mutanen da shugaba Buhari ya aikawa majalisar a ranar Laraba, 01 ga watan Yuli;
1. Umar Sulieman, Adamawa
2. L. S Mandama, Adamawa
3. Oboro Akpabio, Akwa Ibom
4. Elejah Onyeagba, Anambra
5. Abubakar Siyi, Bauchi
6. Philip Ikurusi, Bayelsa
7. Tarzoor Terhemen, Benue
8. Paul Adikwu, Benue
9. Al-Bishir Al-Hussain, Borno
10. Bwala Bukar, Borno
11. Monique Ekpong, Cross River
12. Oma Djebah, Delta
13. Ominyi Eze, Ebonyi
14. Yamah Musa, Edo
15. C. O Ugwu, Enugu
16. Hajara Salim, Gombe
17. Obiezu Chinyerem, Imo
18. Ali Magashi, Jigawa
19. M. A Markarfi, Kaduna
20. Hamisu Takalmawa, Kano
21. Jazuli Gadalanci, Kano
22. Amina Kurawa, Kano
23. Yahaya Lawal, Katsina
24. Dare Sunday Awoniyi, Kogi
25. Ibrahim Laaro, Kwara
26. Abioye Bello, Kwara
27. Zara Umar, Kwara
28. Ademola Seriki, Lagos
29.Henry Omaku, Nasarawa
30. Sarafa Isola, Ogun
31.Nimi Akinkube, Ondo
32. Adejaba Bello, Osun
33. Adeshina Alege, Oyo
34. Debo Adeshina, Oyo
35. Folakemi Akinyele, Oyo
36. Shehu Yibaikwal, Plateau
37. Maureen Tamuno, Rivers
38. Faruk Yabo, Sokoto
39.Adamu Hassan, Taraba
40. Yusuf Mohammed, Yobe
41. Abubakar Moriki, Zamfara
A cikin wata ta daban, shugaba Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da nadin sabbin kwamishinoni uku a hukumar daidaito a rabon mukami da daukan aiyuka a gwamnatin tarayya (FCC).
DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabon shugaban cibiyar kasuwanci ta NEPZA
Kazalika, a wata wasikar mai zaman kanta, shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta amince da nadin kwamshina guda daya da ya yi a hukumar kasafta kudaden rabanu da gwamnatin tarayya (RMAFC).
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng