Aikin shimfida bututun gas da Buhari ya kaddamar zai dawo da martabar Kano a Afrika ta Yamma - Ganduje

Aikin shimfida bututun gas da Buhari ya kaddamar zai dawo da martabar Kano a Afrika ta Yamma - Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi tsokaci kan aikin shimfida bututun iskar gas da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a ranar Talata.

Ganduje ya ce babu shakka wannan katafaren aikin zai hanzarta farfadowar masana'antu a fadin kasar tare da dawo wa kasar martabarta a matsayin cibiyar kasuwanci.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne yayin halartar bikin kaddamar da katafaren aikin daga jihar Kogi wanda shugaban kasa Buhari ya jagoranta a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2020.

Hakan yana kunshe cikin wata sanarwa da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kano, Alhaji Abba Anwar ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa, "da yake shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fahimci matsalar da jihar Kano take ciki, ya gano wajabcin kaddamar da wannan aiki domin dawo da martabar masana'antu a jihar wadda ta kasance cibiya ta kasuwanci."

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin Kano
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya ne shugaba Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas wanda zai fara tun daga Ajaokuta ya ratsa ta Kaduna kuma ya dire a Kano.

Ana sa ran kammala wannan aiki na shimfidar bututun mai tsawon kilomita 614 cikin watanni goma sha biyu.

Wannan aiki na bututun gas mai fadin inci 40, zai rika jigilar iskar gas mai nauyin cubic feet biliyan 2.2 a duk rana.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Hukumar tara haraji ta Kano ta dakatar da mutane 308 daga aiki

Bututun zai taso tun daga Ajaokuta na jihar Kogi, kuma ya ratso ta birnin Abuja zuwa Neja da Kaduna sannan ya tuke a jihar Kano.

Za a batar dala biliyan 2.8 wajen kammala wannan aiki da aka yi wa lakabi da AKK (Ajaokuta-Kaduna-Kano).

Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ne daga nesa yana zaune a fadarsa ta Aso Villa ta hanyar amfani da fasahar taro ta bidiyo, a wani yanayi da 'yan Hausa ke kira 'mai kama-da-wane'.

An kaddamar da aikin ne daga kusurwa biyu tare a lokaci guda, inda Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya wakilci Buhari ta bangaren Ajaokuta tare da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari.

A daya bangaren Kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya kaddamar da aikin daga Rigachikun tare da Karamin Ministan Albarkatun Mai, Cif Timipre Marlin Sylva.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel