'Ya'yan El-Rufai sun caccaki Atiku bayan dan sa ya yi wa El-Rufai habaici
'Ya'yan Gwamna Nasir El-Rufai, Bashir da Bello, sun caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bayan daya daga cikin 'ya'yansa ya yi wa mahaifinsu habaici.
Dan Atiku Abubakar mai suna Mustapha, ya yi martani a inda El-Rufai ke shawartar iyaye da su koyar da 'ya'yansu girmama mata tun suna kanana.
A cewar gwamnan, hakan ne kadai zai iya dakile annobar fyade da ke tashe a kwanakin nan.
Babu kakkautawa Mustapha Atiku ya je yayi tsokaci a kasan wallafar inda yace "Abun mamaki".
Babu jimawa kuwa Bashir El-Rufai ya yi martani inda ya kira sunan Atiku tare da cewa "Irin wannan abun mamakin ne ke faruwa a duk lokacin da mahaifinsa ya yi magana a kan rashawa."
Ba tare da bata lokacin ba, Bello El-Rufai ya je ya yi nasa martanin mai zafi inda yace, "Bash, zancen ana yinsa ne a kan darajar mata ba luwadi ko rashawa ba.
"Kada ka damu da sabon angon, tsohon abokin naka ya yi tunanin a yanzu yana fadar shugaban kasa inda yake da daman kaiwa ga NNPC kai tsaye."

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng