Buhari ya nada sabon shugaban cibiyar NEPZA

Buhari ya nada sabon shugaban cibiyar NEPZA

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Farfesa Adesoji Adesugba a matsayin sabon manajan darektan cibiyar kasuwanci ta NEPZA wacce ke karkashin ma'aikatar kasuwanci da saka hannun jari.

Amincewar shugaba Buhari na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, wacce aka aikawa ministan ma'aikatar a ranar 26 ga watan Yuni, 2020.

Da ya ke sanar da hakan ga manema labarai, Otunba Richard Adeniyi Adebayo, kakakin ministan kasuwanci da saka hannun jari, Mista Julius Toba-Jegede, ya yabawa shugaba Buhari a kan nadin Farfesa Adesoji Adesugba.

Ministan ya nuna jin dadinsa bisa zabin Farfesa Adesugba wanda ya bayyana a matsayin kwararre a bangaren sanin harkokin kasuwanci da ke da gogewa da sanin makamar aiki.

Farfesa Adesugba lauya ne da ke da kwarewa ta musamman a bangaren raya tattalin arziki da habaka harkokin kasuwanci a ciki da wajen Najeriya.

Kafin nadinsa, Farfesa Adesugba ya kasance mai bayar da shawara a kan harkokin shari'a a babbar kungiyar 'yan kasuwa da manoma ta kasa (NACCIMA) sannan kuma malamin jami'a na wucin gadi a wata jami'ar harkokin kasuwanci da ke Dublin a kasar Ireland.

Buhari ya nada sabon shugaban cibiyar NEPZA
Buhari
Asali: Twitter

Kazalika, Adesugba ya kasance malami mai ziyara a kwalejin harkokin kasuwanci da saka hannun jari a makarantar koyar da harkokin kasuwanci ta kasa da kasa da ke Baden a kasar Switzerland.

A nahiyar Afrika, Farfesa Adesugba ya na koyarwa a jami'ar kasar Amurka da ke yammacin Afrika wacce ke birnin Banjul na kasar Gambia.

DUBA WANNAN: Hukumar NIS ta yi karin bayani a kan hanyar daukan aiki, ta garagadi ma su nema

A baya Adesugba ya taba aiki a hukumar gwamnatin tarayya da ke kula da warware rigingimun da kan iya tasowa a tsakanin manyan kamfanonin da ke Najeriya (IAP).

Kazalika, ya taba aiki a hukumar bunkasa harkokin saka hannun jari a Najeriya (NIPC) wacee keda alhakin samar da sabbin tsare - tsare da zasu habaka tattalin arzikin Najeriya.

A tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007, an sauyawa Adesugba wurin aiki daga NIPC zuwa hukumar sayar da kadarorin gwamnati (BPE) inda ya shugabanci sashen talla, sadarwa da harkokin waje.

Farfesa Adesugba ya fara aiki a hukumar kwastam da mukamin sufeto II a shekarar 1982 kafin daga bisani ya ajiye aikin kwastam ya koma NIPC a sheakar 1999.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel