Tattalin arziki: Buhari ya jagoranci wani zama na musamman a fadar shugaban kasa

Tattalin arziki: Buhari ya jagoranci wani zama na musamman a fadar shugaban kasa

- Shugaba Buhari ya jagoranci wani muhimmin zama a fadarsa ta Aso Villa tare da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

- Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, sun halarci taron

-Akwai yiwuwar taron yana da alaka ne da fafutikar da gwamnatin ke yi na farfado da tattalin arziki sakamakon annobar korona da ta janyo koma baya

- An gudanar da taron ne a babban dakin taro na Council Chambers

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, ya kira wani muhimmin taro wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan sa, Ibrahim Gambari suka halarta.

Mun samu wannan rahoto a wani sako da gwamnatin tarayya ta wallafa kan shafinta na Twitter.

Tattalin arziki: Buhari ya jagoranci wani zama na musamman a fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar Hoto; Gwamnatin Najeriya @NigeriaGov
Tattalin arziki: Buhari ya jagoranci wani zama na musamman a fadar shugaban kasa Hakkin mallakar Hoto; Gwamnatin Najeriya @NigeriaGov
Asali: Twitter

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed da Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, suna daya daga cikin kusoshin gwamnatin da suka halarci taron a fadar shugaban kasa.

Sauran wadanda suka halarci taron daga nesa ta hanyar bidiyo sun hadar da 'yan kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki (PEAC) wanda Bismarck Rewane ya ke jagoranta.

'Yan kwamitin sun hadar da; Ode Ojowu, Shehu Yahaha, Muhammad Sagagi, Chukwuma Soludo, Iyabo Masha da Adedoyin Salami.

Akwai yiwuwar wannan muhimmin taro na sirrance da ya gudana a babban dakin taro na Council Chambers, ba ya rasa nasaba da yunkurin gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Sakamakon annobar korona da kuma tasirinta kan farashin danyen mai, masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki, na ci gaba da kawo dabaru masu amfani da za su iya kawar da koma bayan tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Ka zo ka ziyarce mu a birnin Fatakwal - Wike ya roki shugaba Buhari

Babu shakka masu sharhi musamman Bankin Duniya da sauran hukumomi da suka kware a kan kiyasi, sun ci gaba da hasashen cewa, da yiwuwar annobar korono ta kamo hanyar durkusar da tattalin arzikin duniya baki daya.

A bayan bayan nan ne Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya ce tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi uku cikin 100 a wannan shekara, yayin da na kasashe a fadin duniya ke raguwa cikin hanzarin da ba a taba ganin irinsa ba.

IMF ya bayyana durkushewar tattalin arzikin a matsayin mafi muni tun matsin tattalin arziki da aka shiga a duniya a shekarar 1930, wanda ake kira 'Great Depression'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel