FG ta bayyana dalilin karancin mutuwar ma su korona a Najeriya
- Kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona a kasa (PTF) ya bayyana dalilin da ya sa annobar cutar korona ba ta hallaka mutane da yawa
- Shugaban PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, yace mafi yawan wadanda su ka kamu da cutar korona a Najeriya su na tsakanin shekaru 31 zuwa 40
- Mustapha ya bayyana cewa abin mamaki ne yadda Najeriya ke da karancin mutanen da annobar ta hallaka idan aka kwatanta da wasu kasashen kudancin kasar Amurka kamar Brazil
Kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona a kasa (PTF) ya bayyana cewa an samu karancin mutanen da annobar korona ta kashe a Najeriya saboda yawancin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya matasa ne.
Boss Mustapha, shugaban kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya ce mafi yawan wadanda su ka kamu da cutar korona a Najeriya su na tsakanin shekaru 31 zuwa 40, a saboda haka basa fuskantar tsananin rashin lafiya.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Mustapa ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, jim kadan bayan ganawar kwamitin PTF da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa.
DUBA WANNAN: Magu ya bayyana kasar Afrika da mabarnata dukiyar Najeriya suka mayar gida
Ya bayyana cewa ya zama dole 'yan Najeriya su godewa Allah a kan samun karancin mutuwar mutanen da su ka kamu da cutar korona.
Mustapha ya bayyana cewa abin mamaki ne cewa Najeriya ta samu karancin mutanen da annobar cutar korona ta kashe idan aka kwatanta da kasashen kudancin kasar Amurka irinsu kasar Brazil da ke da yanayi iri daya da na Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng