Tsohon shugaban NEPC, Lawal ya rasu

Tsohon shugaban NEPC, Lawal ya rasu

Tsohon shugaban riko na Hukumar Inganta Kasuwanci na ƙasa da ƙasa, Mohammed Lawal ya rasu.

Babban ɗansa, Mohammed, ya ce marigayin ya rasu a ranar Alhamis a babban Asibitin Wuse da ke Abuja.

Ya ce ya rasu ne sakamakon buguwar zuciya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon shugaban NEPC, Lawal ya rasu
Tsohon shugaban NEPC, Lawal ya rasu
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, Lawal ne shugaban kamfanin AML Global Trade Ltd.

DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-ɗumi: Buhari ya naɗa sabon jami'i mai kare lafiyarsa

Ya kuma yi aiki a matsayin mamba na Makarantar Nazarin Kasuwanci na Legas.

Har ila yau, marigayi Lawal mamba ne a Hukumar Inganta Kasuwanci na Legas da Abuja.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa Allah ya yi wa babban alkalin jihar Kogi, Nasir Ajanah rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a cibiyar killace masu jinyar cutar COVID-19 da ke Gwagwalada a Abuja kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wani daga cikin iyalansa ya kuma tabbatar wa majiyar Legit.ng rasuwarsa a safiyar yau.

Daya daga cikin hadiman gwamna Yahaya Bello na jihar shima ya rasu a wani asibiti da ke Abuja a cikin kwanakin baya bayan nan.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo bai amsa tambayar da aka masa ba a kan rasuwar amma sakataren watsa labaran gwamnan, Mohammed Onogwu ya sada majiyar Legit.ng da iyalan Ajanah.

Ya ce, "Sune za su fara bayar da sanarwa game da rasuwar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel