Boko Haram ta bukaci $500,000 kudin fansan ma'aikatan tallafi 5 da aka sace

Boko Haram ta bukaci $500,000 kudin fansan ma'aikatan tallafi 5 da aka sace

Wasu yan ta'addan Boko Haram sun bukaci $500,000 kafin su saki ma'aikatan tallafi 4 da maigadi 1 da suka sace bayan bidiyon da aka saki inda ma'aikatan suke rokon gwamnatin tarayya ta kawo musu dauki.

A wannan faifen bidiyo mai tsawon mintuna uku da dakika 37, an ga wadannan ma’aikata da ke tsare su na kira ga hukumomi da gwamnati su ceto su daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.

Daga cikin ma’aikatan da aka cafke har da masu aiki da kungiyoyin Action Against Hunger da Rich International, International Rescue Committee, da kuma wani jami’in gwamnatin Borno.

Wannan bidiyo ya shiga hannun jaridar Daily Trust kamar yadda mu ka samu labari a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, 2020.

Daya daga cikin masu alaka da yan ta'addan kuma yake musu cinikayya ya bayyanawa DailyTrust cewa kungiyar ta bukaci dalar Amurka 500,000 kafin su saki ma'aikatan.

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun amshi cin hancin N44bn yayin dokar kulle a fadin tarayya

Ga jerin sunayen ma'aikatan bada agajin da aka sace:

1. Abdulrahman Dungus wanda ke tare da ‘Rich International’

2. Mai gadi mai suna Joseph Prince

3. Ishaiku Yakubu, wanda jami’i ne da kungiyar ‘Action Against Hunger’

4. Luka Filubus da ke aiki da kungiyar ‘International Rescue Committee’ a Munguno

5. Abdulrahman Babagana, jagoran hukumar bada agaji na SEMA a garin Monguno

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel