Coronavirus: Matakai 8 da gwamnatin tarayya ta sake dauka na sassauta dokar kulle

Coronavirus: Matakai 8 da gwamnatin tarayya ta sake dauka na sassauta dokar kulle

A yau Litinin, 29 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta amince da sake sassauta dokar kulle a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin Kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona a kasa (PTF) da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamitin ya sake komawa gaban shugaba Buhari domin gabatar ma sa da sabbin bayanai dangane da yaki da annobar.

Kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa yayin ganawa da Buhari
Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa yayin ganawa da Buhari Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Tun bayan gabatar masa da bayanai, an sa ran cewa za a sanar da sabbin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin ci gaba da sassauta dokar kulle.

Kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya; Boss Mustapha yake jagoranta ya hadar da; ministan lafiya; Osagie Ehanire, jagoran kwamitin; Dakta Sani Aliyu, da shugaban hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu.

KARANTA KUMA: Buhari zai kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas na AKK a ranar Talata

Biyo bayan haka ne gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu ga 'yan ajin karshe na makarantun firamare da na sakandire a fadin kasar nan.

A yunkurin da ta ke yi na sassauta dokar hana walwala, gwamnatin cikin matakan da ta dauka ta kuma cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.

Sauran matakan da gwamnatin ta shata sun hadar da;

Gwamnatin ta amince da dawo da zirga-zirgar jiragen saman cikin gida.

Bude makarantu ga dalibai 'yan aji shida na makarantun firamare da kuma 'yan SS3 da JS3 na makarantun sakandire.

Gidajen cin abinci za su ci gaba da kasance a rufe.

Wuraren haska fina-finai wato Silimia, da wuraren motsa jiki za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Mutum 20 kawai aka amincewa su halarci daurin aure ko kuma jana'iza.

Amfani da takunkumin rufe fuska ya zama wajibi a cikin taron jama'a.

Ma'aikatan gwamnati za su ci gaba da fita aiki daga karfe 9.00 na safiya zuwa 2.00 na rana daga Litinin zuwa Juma'a babu fashi.

Tanadar wuraren wanke hannu da sabulu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin tsaftace hannu wato sanitizer a wuraren taron jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel