An fasa kara farashin wutar lantarki a Najeriya

An fasa kara farashin wutar lantarki a Najeriya

Majalisar dattijai ta sanar da cewa ta samu nasarar shawo kan kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki (DisCos) a kan yunkurinsu na kara kudin wutar da su ke bawa jama'a.

A cikin wani jawabi, Ola Awoniyi, kakakin shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya ce an cimma yarjejeniyar janye karin wutar yayin taron shugabancin majalisa da wakilan DisCos

Tun a cikin wtan janairu, hukumar kula da rarraba hasken wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta sanar da cewa za a kara kudin wutar lantarki a fadin kasar nan daga ranar 1 ga watan Afrilu.

Amma sai sanarwa ta fito daga NERC a cikin watan Maris wacce ta umarci DisCos su dakatar da kara farashin wutar lantarki saboda bullar annobar korona.

An fasa kara farashin wutar lantarki a Najeriya
Ahmed Lawan
Asali: Facebook

Daga bisani, ministan wutar lantarki, Sale Mamman, ya ce sabon karin farashin wutar lantarkin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuli.

DUBA WANNAN: EFCC: Kotu ta yi barazanar janye belin tsohon Sanata Shehu Sani

Yayin zaman da aka yi tsakanin shugabancin majalisar dattijai da sauran ma su ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki, an lallami DisCos sun hakura da batun karin har sai zuwa farkon shekarar 2021 saboda annobar korona.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin tarayya ta ce za a cigaba da rufe makarantun kananan yara da makarantun firamare da ke fadin kasar nan.

A sanarwar da ta fito kafin wannan, gwamnatin tarayya ta ce za a bude makarantu daga matakin firamare zuwa sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da Dakta Sani Aliyu, jagoran kwamitin yaki da annobar korona a kasa, ya fitar a Abuja ya ce ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba.

"Ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba har sai sanarwa ta gaba," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel